✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta kafa kwamitin Gwamnoni 6 don inganta rayuwar matasa

Kwamitin ya kunshi Gwamnoni 6 da aka zaba daga duk shiyya cikin shiyyoyin siyasar kasar.

Fadar Shugaban Kasa ta kafa wani sabon kwamiti mai dauke da Gwamnoni shida da zai jibinci lamarin sauraro da biyan bukatun matasan kasar biyo bayan zanga-zangar da ta rikide zuwa rikici da aka shafi kwanaki ana yi a fadin kasar.

Fadar Shugaban Kasar ta bayyana hakan ne cikin wani sako da wallafa a shafinta na Twitter da cewa Kwamitin zai samar da matakan hadin gwiwa a tsakaninta da Gwamnatocin Jihohi domin yin nazari da shimfia tsare-tsaren kawo karshe zanga-zangar EndSARS da kuma mafita ta inganta tsaron kasa.

Gwamnatin Tarayyar ta yanke hukuncin hakan ne bayan taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da aka gudanar a ranar Litinin, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo jagoranta kamar yadda ya saba.

Kwamitin wanda Mataimakin Shugaban Kasar zai jagoranta ya kunshi Gwamnoni shida da aka zaba daga duk shiya cikin shiyyoyin siyasa shida dake fadin kasar.

Gwamnonin da aka zaba sun hadar da na Sakkwato daga shiyyar Arewa ta Yamma, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Borno daga shiyyar Arewa ta Gabas, Babagana Zulum da Gwamnan Neja daga shiyyar Arewa ta Tsakiya, Abubakar Sani Bello.

Sauran su ne Gwamnan Ondo daga shiyyar Kudu maso Yamma, Rotimi Akeredolu da Gwamnan Ebonyi daga shiyyar Kudu maso Gabas, David Nweze Umahi da kuma Gwamnan Jihar Delta daga shiyyar Kudu maso Kudu, Ifeanyi Okowa.

Kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta bayyana, Kwamitin zai fara aiki nan take, inda zai mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin inganta rayuwar matasa ta hanyar yin aiki tare da Kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai.