✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalar zikiri (4)

Wannan wurin zikiri da dambaton Allah ke nan. Wannan falalar zikiri ne da ladansa. Duk wurin da ba a ambaton Allah to hasara ne ga…

Wannan wurin zikiri da dambaton Allah ke nan. Wannan falalar zikiri ne da ladansa. Duk wurin da ba a ambaton Allah to hasara ne ga ma’abota zamansa! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ina masu bata lokacinsu wajen zama a wuraren kallon kwallo suna iface-iface da zage-zage? Ina masu bata lokacinsu a wuraren wasanni da ludo da sunuka da dara da wuraren kade-kade da raye-raye? Ku duba julma ta karshe na wannan Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya ruwaito Ubangijinsa Yana cewa: “Su (masu zikiri da ambaton Allah da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan da’a ga Allah) masu zama ne da duk wanda ya zauna da su ba zai tabe ba.”

Don haka kowane mutum ya rika duba abokan zamansa, ya rika duba abin da harsunansu sukefurtawa, ya rika lura da abin da kunnunwansa za su rika saurare daga gare su. Idan ya kasance ambaton Allah ne da tunawa da Shi, to sai ya sani yana tare da masoya Allah Madaukaki. Imam Ghazali (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Idan mutane suka zauna a wani wurin zama, to kowa yana magana ne a kan abin da yake so. ’Yan kasuwa suna magana ne kan kasuwancin, kafinta yana magana ne a kan katako da kofofi da gadaje, makeri yana magana ne a kan karafa da abin da suka shafe su. Likita yana magana ne a kan magunguna da jinya da cututtukan da suke damun mutane. Injiniya yana magana ne a kan gini da tsara hanyoyi, yayin da mai dukiya yake magana a kan dukiya da shaguna da motoci ko jiragen ruwa da na sama da kamfanoninsa. Su kuma masoya Allah lallai su a duk inda suka zauna maganarsu ta farko ita ce tunawa da ambaton Allah Mai tsarki da daukaka, kuma karshen maganarsu ita ce tunawa da ambaton Allah Madaukaki. Don haka ne wurin zamansu ya kasance lambu ne daga cikin lambunan Aljanna.”

Shi ya sa Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Idan kuka zo wucewa ta lambun Aljanna ku tsaya.” Ma’ana ku zauna a cikinsa ku amfana da abin da ke cikinsa. “Sai suka ce. “Mene ne lambun Aljanna?”  Shin a duniya akwai Aljanna ce? Mu lallai mun san Aljanna a Lahira take to ina ne lambun Aljanna a duniya? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wuraren da ake ambaton Allah (zikiri da karatun Alkur’ani da wa’azi da duk abin da ya shafi tunatar da mutane hukunce-hukuncen addini). Su ne lambunan Aljanna a duniya kafin a je Lahira. 

Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wadansu mutane da za su taru a wani wurin zama sannan su rabu ba tare da sun ambaci Allah Madaukaki ba a wurin zaman nasu face wannan wurin zama ya zame musu hasara a Ranar kiyama.” 

Zikiri da ambaton Allah ibada ce mai sauki, mutum zai iya yin ta yana tsaye ko yana kishingide ko yana tafiya a kafa ko a jirgin ruwa ko a cikin mota ko yana zaune a gidansa ko yana kan hanyarsa ta zuwa wani wuri ko yana zaune a shagonsa na kasuwa ko yana cikin ofis yana gudanar da aikinsa ko yana tura baro ko yana sanya fasinja a mota ko yana kwaba yashi da siminti domin gini ko yana dora bulo a yayin gini ko mace tana tuyar kosai ko dama koko ko dafa abinci ko tana yi wa yara wanka ko tana dinki a kan keke ko tana saka ko tana shara a kowane hali mutum zai iya zikiri ya ambaci Allah. Annabi (SAW) ya kasance yana ambaton Allah yana zikiri a cikin dukan halayen da ya samu kansa. Kuma duk lokacin da bawa ya ambaci Allah ya tuna da shi ya yabe shi duk muhallin da ya yi wannan ambato ko zikiri ko yabo in dai ya yi ne domin neman yardarm Allah, ba domin riya ko don a ji ba, wannan muhalli zai yi masa shaida a Ranar kiyama. “A wannan ranar (kasa) tana bayar da labarinta. Domin lallai Ubangijinka Ya yi mata wahayi (ishara).” (Az-Zilzila: 4-5).

Bisa lura da irin wannan falala ta zikiri da ambaton Allah da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan tunawa da Allah, wane irin tabewa da gafala ne za su sanya mutum ya rafkana a ce rana ta fito ta fadi bai ambaci Allah da yawa ta wajen yin azkar din da muka ambtao a baya ba?

Duk wanda yake gafala daga ambaton Allah da zikiri da karatun Alkur’ani hakika yana nakasa rayuwarsa ce da rusa darajarsa da girmansa a gaban Allah Madaukaki. Annabi (SAW) ya ce kamar yadda Abu Dawud ya ruwaito daga Hadisin Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya zauna a wani wurin zama amma bai ambaci Allah ba, sai wannan wurin zama ya zame masa tirratun daga Allah. Haka wanda ya kwanta a wani wurin kwanciya amma bai ambaci Allah a cikinsa ba, zai zame masa tirratun daga Allah.) Tirratun shi ne kamu na hukunci da nakasa. Haka lamarin yake a ce mutum yana tafiya zuwa wani wuri amma ba ya ambaton Allah a yayin wannan tafiya.

Wata falala ta zikiri ita ce yin zikiri yana kara karfin hankalin mutum ya ba shi kaifin basira da kwakwalwa da karfin jiki. Dalili wata rana Fadima (Allah Ya kara mata yarda) ta zo wurin Annabi (SAW) tana bukatar ya ba ta mai yi mata hidima domin ta taimaka mata wajen ayyukan gida, domin tana gajiya daga ayyukan nika da girki da debo ruwa da sauran hidimar gida. Sai ta zo wurin mahaifinta (SAW) ta ce ta nemi mai yi mata hidima amma ba ta samu ba, sai ta fada wa A’isha (Allah Ya kara mata yarda) cewa ga abin da ya kawo ta, sannan ta koma gidanta. Lokacin da Annabi (SAW) ya zo, sai A’isha (RA) ta ba shi labarin abin da Fadima (RA) take nema. Sai Annabi (SAW) ya tafi gidan su Fadima (RA) tana shirin kwanciya ita da mijinta Aliyu bin Abu dalib (Allah Ya kara masa yarda). Sai Annabi (SAW) ya ce da su: “Shin ban a sanar da ku mafi alherin abin da kuka nema ku biyun ba? Ku yi takbiri sau talatin da hudu, ku yi tasbihi sau talatin da uku ku yi tahmidi sau talatin da uku.” Wato idan za ku kwanta ku yi kabbara sau 34 ku yi tasbihi sau 33 ku yi tahmidi sau 33, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wannan ya fiye muku alheri daga mai yi muku hidima.”

Kan haka ne Ibn kayyim (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Wanda ya dauwama a kan zikiri, – ma’ana a kan wannan zikiri – a lokacin da zai kwanta barci zai samu karfin jiki da zai wadatar da shi daga mai yin hidima.” 

Wani zikiri mai falala kuma shi ne fadin “Lahaula wala kuwatta illa billah.” An ce lokacin da Allah Madaukaki Ya halicci masu daukar Al’arshi Ya umarce su da su dauki Al’arshin, sai suka ce: “Wane ne zai iya daukar Al’arshin ya Ubangiji! Sai Ubangiji Madaukaki Ya ce: “Ku ce: “Lahaula wala kuwatta illa billah.” Sai suka ce: “Lahaula wala kuwatta illah billah, sai suka dauke shi (Al’arshin).”

Ibn kayyim ya ce: “Wannan kalma: Lahaula wala kuwatta illa billah tana da tasiri mai ban mamaki wajen magance abubuwa masu wahala da daukar abubuwa masu nauyi. Don haka idan al’amari ya yi maka tsanani ko wani abu ya yi maka nauyi ka ce: Lahaula wala kuwatta illa billah.”

Wannan kadan ne daga falalar zikiri da ambaton Allah, don haka a gwamutsi malamai don samun bayani a kai.

Ya wajaba ga Musulmi musamman matasa su guji gafala da sauraren kade-kade da wake-wake da wuraren wasanni,  su sabar wa kawunansu yawaita fadin “Subhanallah walhamdulillah, wa la’ilaha illallah wallahu akbar, wala haula wala kuwatta illah billah.” Su ne kyawawan ayyuka masu tabbata, kuma su ne suke gyara zukata su fadada su, su rika nishadi da jin dadi.

Allah Ya sanya mu daga cikin masu yawan ambatonSa. Ya sanya mu daga cikin masu yawan gode maSa, masu yawan yi maSa tasbihi.

Wasallallahu wa sallim ala Sayyidina Muhammad