✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Falasdinu ta janye daga kungiyar kasashen Larabawa

Falasdin ta janye daga jagorantar tarukan Kungiyar Kasashen Larabawa ta Arab League. Ministan Harkokin Wajen Falasdinu, Riyad al-Maliki, ya sanar da hakan a ranar Talata,…

Falasdin ta janye daga jagorantar tarukan Kungiyar Kasashen Larabawa ta Arab League.

Ministan Harkokin Wajen Falasdinu, Riyad al-Maliki, ya sanar da hakan a ranar Talata, yana kuma sukar yarjejeniyoyin diflomasiyya tsakanin kasashen Larabawa da Isra’ila a matsayin cin mutunci kuma abin kunya.

“Falasdin ta yanke shawarar sarayar da damarta na jagorantar Majalisar Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar da za a yi nan gaba.

“Sam babu mutunci a yadda Larabawa ke ta rububin mayar da hulda da Isra’ila a daidai lokacin da kasarmu ke jagorantar tarukan”, inji Maliki.

Falasdinawa na ganin yarjeniyoyin da Hadaddiyyar Daular Larabawa da kuma Bahrain suka rattaba hannu tsakaninsu da Isra’ila a birnin Washington na Amurka a makon jiya a matsayin cin amana ga fafutikar da suke yi; sa’annan wata mahangurba ce ga yunkurinsu na kafa ’yantacciyar kasar Falasdinu a yankunan da Isra’ilar ta mamaye.

A farkon watan nan, Falasadinawan sun  gagara shawo kan kungiyar ta Arab League ta yi tofin tir da kasashen da suke kokarin mayar da huldar diflomasiyya da kasar Yahudun.

Falasdin dai ita ce ya kamata ta jagoranci tarukan kungiyar na wata shidan da ke tafe, amma Minisatn Harkokin Wajenta Riyad al-Maliki ya fada wa wani taron manema labarai a birnin Ramallah na Zirin Gaza da ke karkashin mamaya, cewa Falasdinu ba ta bukatar wannan matsayin a yanzu.