✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin garin rogo zai tashi saboda faduwar damina a Kuros Riba

An yi hasashen farashin garin rogo da aka fi sani da kwaki, zai yi tashin gauron zabi a Jihar Kuros Riba, sakamakon damina ta fadi,…

An yi hasashen farashin garin rogo da aka fi sani da kwaki, zai yi tashin gauron zabi a Jihar Kuros Riba, sakamakon damina ta fadi, an koma gona, duk da yadda manoman rogo suka tashi haikan kan nomansa a fadin jihar.
 Kwamishinan ma’aikatar gona, James Aniom  ne ya bayyana haka ganawar da ya yi da manema labarai a Kalaba, kuma ya ce manoman sun hango alfanun noman rogon ne, musamman da yanzu an koma hatta burodi ana yi da fulawar rogo.
Ya ce sannan ga gwamnati tana tallafa wa kungiyoyin manoma da rancen kudi da magungunan kwari don feshi a gonakinsu.
Binciken da Aminiya ta gudanar a garuruwan Ugep da Ogoja da kuma Kalaba, ya nuna farashin ya soma tashi.
Madam Grace Efffah, shugabar kungiyar masu sayar da garin rogo ta bayyana matsalar sufuri da rashin kyawun hanyoyi sun haifar da tashin farashin, sannan “Manona yanzu damina ta fadi, an koma gona, saboda haka ba lokaci sarrafa rogo, shi ya sa yadda hankali ya koma gona, dole garin kwaki ya yi tsada”. Inji ta.