✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Bande ya zama Shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jakada Tijjani Muhammad Bande ya zama sabon Shugaban Zauren Majalisar a zaman Majalisar kashi na 74. Frfesa…

Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jakada Tijjani Muhammad Bande ya zama sabon Shugaban Zauren Majalisar a zaman Majalisar kashi na 74.

Frfesa Bande, wanda da ma ya taba tsayawa takarar wannan mukamin, an zabe shi ne a Talatar da ta gabata, a wani zama na musamman da Majalisar ta yi a Birnin New York.

Shugaban, wanda zai kama aiki a cikin watan Satumba mai zuwa shi ne dan Najeriya na biyu da ya taba rike wannan mukami wato bayan tsohon Jami’in Soja kuma tsohon Jami’in Diflomasiyya Joseph Garba wanda ya jagoranci wannan Majalisa tun a shekarar 1989 zuwa 1990. Ma’aikatar Harkokin wajen Najeriya ta bayyana farin cikinta ga wannan nasara da Bande ya samu, inda ta bayyana cewa wannan wata alama ce mai nuna ’Yan Najeriya suna da kimar da za su jagoranci wasu Hukumomi na Kasa da kasa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya tabbatar wa sabon shugaban cikakken goyon bayansa domin ya aiwatar da ayyukansa tare da cin ma muhimman kudurorinsa.