Search
Subscribe
Fargabar Kurona: Ya kulle matarsa a ban-daki

Fargabar Kurona: Ya kulle matarsa a ban-daki

Kafafen watsa labarai a kasar Lithuania sun ruwaito  cewa, wani abin da ba a saba gani ba, ya auku, inda wani mutum ya kulle matarsa a cikin ban-daki saboda fargabar za ta kamu da cutar Kurona da ke barna a sassan duniya.

A ranar Laraba, 26 ga Fabrairu ne, ’yan sanda a garin Bilnius na kasar Lithuania suka ce matar ta kira su inda ta shaida musu cewa, mijinta ya kulle ta a ban-daki.

’Yan sandan sun yi kokari sun adireshin gidan. Da suka isa gidan, sun gano cewa ba fada ba ne ya shiga tsakanin matar da mijinta. Mijin ya shaida wa ’yan sandan cewa, ya kulle matarsa ce saboda ya kare ta daga kamuwa da cutar Kurona.

Mai magana da yawun ’yan sandan, Ramunas Matonist, ya fada wa ’yan jarida a yankin cewa, “Mun samu rahoton cewa wani mutum da ’ya’yansa biyu sun kulle matar a ban-daki inda suka hana ta fita saboda ta ce  musu saura kadan ta kamu da cutar Kurona.”

Matar dai ta yi bulaguro zuwa kasar Italiya inda ta yi hulda da wadansu mutanen kasar China, a dalilin haka ne ya sa ta ce wa, mijinta tana tsoron zat a iya kamuwa da cutar Kurona. Amma maimakon mijin ya rarrashe ta, sai ya kira likita ya shaida masa halin da ake ciki.

Likitan ya shawarce shi da ya killace matar, hakan ya sa ya yanke shawarar kulle ta a ban-daki.

Mutumin dai ya bayyana cewa, ya yi haka ne ba don ya cutar da matar tasa ba, sai dai biyayya kawai yake yi ga umarnin likitan saboda kiyaye yaduwar cutar. Babu dai alamar duka a jikin matar, hakan ya sa likitoci suka dauke ta suka kai ta wurin gwaje-gwaje saboda gano ko tana dauke da cutar.

Gwaje-gwajen dai sun nuna cewar matar ba ta dauke da cutar ta Kurona. Wannan labarin yana daya daga cikin labaran da ke nuna yadda jama’a suke tsorata da cutar Kurona (Cobid-19) da kuma yadda jama’a da dama ke fargabar yaduwar cutar, musamman yadda ma’aurata ke fargaba har ta kai miji zai iya kulle matarsa a ban-daki saboda tsoon kamuwa da cutar.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin