✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 2

Babi na Talain da Biyu: Yin kaho da hukuncin amai a cikin Ramadan. Yahya dan Salih ya fada mini ya ce, Mu’awiyya dan Salam ya…

Babi na Talain da Biyu:

Yin kaho da hukuncin amai a cikin Ramadan. Yahya dan Salih ya fada mini ya ce, Mu’awiyya dan Salam ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba mu labari daga Amru dan Alhakam dan Sababan ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Idan mai azumi ya yi amai bai karya azumi ba, domin fita ya yi ba hadeyi shi ya yi ba.” An ambato daga Abu Huraira cewa: “Lallai shi ya ce, haka na karya azumi amma maganar farko shi ya fi inganci.” danAbbas da Ikramata sun ce: “Azumi na karyewa ne ga abin da ya shiga (makoshi) ban da abin da ya fita.” dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya kasance yana yin kaho alhali yana azumi. Sa’an nan daga baya ya bar shi sai ya kasance yana yi da dare.” Abu Musa ya kasance yana yin kaho da dare.” An ambato daga Sa’ad da Zaid dan Arkam da Ummu Salma cewa: “Lallai su, sun yi kaho suna azumi.” Bukair ya ce, daga Ummu Alkamata: “Mun kansance muna yin kaho a wurin A’isha ba ta hana mu.” An ruwaito daga mutane ba daya ba cewa; (Annabi) ya ce, “Mai kaho da wanda aka yi masa azuminsu ya karye.” Ayyashu ya fada mini Abdul A’ala ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Alhassan misalinsa, sai aka ce masa daga Annabi (SAW) kuwa? Ya ce, “Na’am,” sa’an nan ya ce, “Allah dai Shi ne Mafi sani.”

398. An karbo daga Mu’allah dan Asad ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari daga Ayyub daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi kaho yana da Harami kuma ya yi kaho yana azumi.”

399. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdul Waris ya ba mu labari ya ce, Ayyuba ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi kaho alhali yana azumi.”

400. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Na ji Sabitul Bunyani ya ce: “Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Shin kuna kyamar yin kaho ga mai azumi? Ya ce, “A’a, face saboda raunin (jiki).” Shababata ya kara da cewa: Shu’aba ya ba mu labari a zamanin Annabi (SAW).”

 Babi na Talatin da Uku: Yin azumi da shan ruwa a tafiya

 401. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Abu Is’hak Shaibani ya ce: Ya ji dan Abu Aufah (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance tare da Manzon Allah (SAW) a cikin wata tafiya sai ya ce ga wani mutum, sauka ka kwaba mini garin alkama.” Sai ya ce, “Ya Manzon Allah! Da rana (ba ta buya ba)? Ya ce, “Sauka ka kwaba mini alkama.” Ya ce, “Ya Manzon Allah! Da rana! Ya ce, “Sauka ka kwaba mini garin alkama.” Sai ya sauka ya kwaba masa ya sha, sa’an nan ya yi nuni da hannunsa ta nan, sai ya ce; “Idan kuka ga dare ya fuskanta (tafi) daga nan, to, lallai mai azumi ya sha ruwa.” Jarir ya biye masa da Abubakar dan Ayyash da Shaibani daga dan Abu Aufa ya ce: “Na kasance tare da Annabi (SAW) a cikin wata tafiya.”
402. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba ni labari daga Hisham ya ce, Babana ya ba ni labari daga A’isha (RA) cewa: “Lallai Hamza dan Amrul Aslami ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai ni na kasance ina azumi kullum.”