✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fassarar Sheikh Is’hak Yunus Almashgool, Bauchi 3

Babi na Arba’in da Biyu: Wanda ya mutu da azumin wata guda a kansa. Alhassan ya ce, “Idan mutum talatin suka yi masa azumi dai-dai…

Babi na Arba’in da Biyu: Wanda ya mutu da azumin wata guda a kansa. Alhassan ya ce, “Idan mutum talatin suka yi masa azumi dai-dai ya halatta.”
412. An karbo daga Muhammad dan Khalid ya ce: “Muhammad dan Musa dan A’ayan ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari daga Amru dan Haris daga Abdullahi dan Abu Ja’afar cewa: “Lallai Muhammad dan Ja’afar ya ba shi labari daga Urwata daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya mutu da azumi a kansa, waliyyinsa yana iya yin masa azumin.” dan Wahab ya biye masa daga Amru, Yahaya dan Ayyub ya ruwaito shi daga dan Abu Ja’afar.

413. An karbo daga Muhammad dan Abdurrahim ya ce: “Mu’awiya dan Amru ya ba mu labari ya ce, Za’idata ya ba mu labari daga A’amashi daga Muslim Badin daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Wani mutum ya zo ga Annabi (SAW) sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai Uwata ta mutu da azumin wata daya a kanta, shin zan iya biya mata? Ya ce, “Na’am, bashin Allah shi ya fi cancanta da biya.” Sulaiman ya ce, “Hakamu da Salmata, suka ce, “Muna zaune gaba daya lokacin da Muslim ya ba da wannan labari,” suka ce, “Mun ji Mujahid yana ambatawa daga dan Abbas……..cewa: “Wata mace ta ce wa Annabi (SAW) cewa: Uwata ta mutu ana bin ta azumin kwana goma sha biyar.”

Babi na Arba’in da Uku: Yaushe ya halatta ga mai azumi ya yi buda baki? Abu Sa’idul Khudri ya yi buda baki lokacin da kwanson rana ya buya.”
414. An karbo daga Humaid ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Hisham dan Urwat ya ce, “Na ji Babana yana cewa: “Na ji Asim dan Umar dan Khaddab daga Babansa (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan dare ya fuskanci ta nan, yini ya juya daga ta nan. Kuma rana ta buya, to mai azumi zai yi buda baki.”
415. An karbo daga Is’hak Alwasidiyyu ya ce: “Khalid ya ba mu labari daga Shaibani ya ba mu labari daga Abdullahi dan Abu Aufa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a cikin wata tafiya yana azumi. Lokacin da rana ta buya, sai ya ce, ga wasu mutane: Ya wane! Sauka ka kwaba mana garin alkama da ruwa.” Sai ya ce, “Ya Manzon Allah! Da rana da dai ka yini,” ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama da ruwa,” ya ce, “Ya Manzon Allah! Da dai ka yini,” ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama,” ya ce, “Da sauran yini.” Ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama, sai ya sauka ya kwaba musu. Annabi (SAW) ya sha sa’an nan ya ce: “Idan kuka ga dare ya fuskanci ta nan to, lallai mai azumi ya yi buda baki.”
 
Babi na Arba’in da Hudu: Mai azumi yakan iya buda baki da abin da ya saukaka daga ruwa ko wani abu:
416. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abdulwahid ya ba mu labari ya ce, Shaibani ya ba mu labari ya ce, “Na ji Abdulllahi dan AbU Aufa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Mun fita tare da Manzon Allah (SAW) lokacin yana azumi. Lokacin da rana ta buya ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama.” Sai mutumin ya ce, “Ya Manzon Allah! Da dai ka yini.” Ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama.’ Ya ce, “Ya Manzon Allah! Lallai da sauran yini.” Ya ce, “Sauka ka kwaba mana garin alkama.” Sai ya sauka ya kwaba. Sa’an nan (Annabi) ya ce, “Idan kuka ga dare ya fuskanci ta nan, to, lallai mai azumi ya yi buda baki, ya yi nuni da yatsunsa ta wajen gabas.”