Da Dumi Dumi

Faston da ya yi garkuwa da kansa ya shiga hannu

Dubun wani faston coci a jihar Ekiti ta cika bayan da ya shirya yin garkuwa da kansa domin karbar kudin fansa daga mabiyan cocinsa.

Faston mai suna Rabaran Adewuyi Adegoke ya kitsa yin garkuwar karya da kansa ne, ya hada baki da karin wasu mutane da wani mutum wanda shi ya tuntubi mabiyan cocin Faston inda ya nemi su biya kudin fansa Naira miliyan uku.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi nasarar kame wanda ya yi waya da mabiya cocin da aka nemi su biya kudin fansar

Daga dama Faston da ya shirya garkuwa da kansa tare da wanda ya-kira waya domin karvar-kudin fansa.

bayan da suka gano inda yake ta hanyar bibiyar layin wayar salular sa inda nan take ya bayyana cewa, Faston ne ya kintsa yin garkuwa da kansa domin karban kudin fansa daga mabiyansa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti CP Amba Asuquo, ya shaida cewa rundunar na kan binciken lamarin.

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya