Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sha kunya a hannun Lobi Stars ta Benuwai bayan da ta biyo ta har gida ta mata ci daya main ban haushi a gasar Firimiyar Najeriya. Dan wasan Lobi Stars Douglas Achib ne ya zira kwallon cikin minti na 62.
Karo na biyu ke nan da Pillars take tashi ba tare da samun nasara ba; ta yi canjaras daya kuma an doke ta a sau daya. Yanzu haka Pillars na mataki na 17 a teburi da maki daya kacal. Ita kuwa Lobi Stars tana mataki na biyar da maki shida. Ga wasu sakamakon wasannin da aka buga.
Abia Warriors 1 – 1 Sunshine Stars
Delta Force FC 4 – 1 Jigawa Golden Stars
Enugu Rangers 0 – 1 MFM FC
Enyimba 3 – 1 Akwa United
Heartland Owerri 1 – 1 Akwa Starlets
Ifeanyi Ubah United 1 – 0 Ribers United FC
Katsina United 1 – 0 Nasarawa United
Plateau United 2 – 1 Wikki Tourist
Warri Wolbes FC 2 – 0 Adamawa United