✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fuskokin wadanda ake zargi da hannu a bacewar Janar Alkali

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta ayyana neman Dagacin Dura Yakubu Rap da wadansu mutum bakwai ruwa-a-jallo sakamakon ganowar da ta yi cewa suna da…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta ayyana neman Dagacin Dura Yakubu Rap da wadansu mutum bakwai ruwa-a-jallo sakamakon ganowar da ta yi cewa suna da hannun wajen bacewar Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya).

Rundunar ’Yan sandan wadda ta fitar da hotunan wadanda ake zargin ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa wadanda take nema ruwan suna da hannu wajen kitsawa da garkuwa da kuma bacewar Janar Alkali da aka daina jin duriyarsa tun a ranar 3 ga Satumban bana.

Rundunar ta annaya sunayen mutanen da ake zargin ne a wata sanarwar dauke da sa hannun Kakakinta, DSP Tyopeb Terna da ta fitar a shekaranjiya Laraba.

Ta ce Dagacin Dura Du gundumar da ake zargin a nan Janar Alkali ya bace, Mista Yakubu Rap, baki ne mai kimanin shekara 52, yana da aure da ’ya’ya kuma dan kibilar Berom ne da yake magana da Hausa da Ingilishi.

Sauran su ne Da Chuwang Samuel wanda aka fi sani da Mourinho, mai shekara 28, baki, dogo, ba ya da zane a fuska, dan kabilar Berom da ke iya magana da Hausa da Ingilishi. Akwai Nyam Samuel da ake kira da Soft Touch, mai shekara 25, dogo ne baki, ba ya da zane a fuska. Soft Touch yana aikin gyaran mota, kuma dan kabilar Berom da ke iya magana da Hausa da Igilishi sosai. Sai Mathew Wrang da ake kira da Amesco, mai shekara 27, dogo ne baki, kuma ba ya da zane a fuska. Yana da zakaran wuya, yana da aure, kuma dan kabilar Berom ne, yana magana da Hausa da Ingilishi sosai.

A cikin wadanda ake neman akwai Pam Gyang Dung mai lakabin Boss, mai kimanin shekara 53, kuma ba ya da wasu hakoran sama. Baki ne dogo ba ya da zane a fuska, yana da sanko, manomi ne da yake sana’ar hakar ma’adani. Dan kabilar Berom ne, yana magana da Hausa da Ingilishi da harshensa na Berom. Sai Chuwang Istifanus Pwajok Stephen mai lakabin Tifa, mai shekar 46, fari ne mai gemu kuma dogo, ba ya da zane a fuska. Dan kasuwa ne kuma mai aikin safiyo (surbeyor), dan kabilar Berom ne da ke magana da Hausa da Ingilishi.

Sai Timothy Chuan mai shekara 26, dogo ne fari, ba ya da zane a fuska yana da aure kuma yana tuka tifar dibar yashi. Dan kabilar Berom ne, kuma yana magana da Hausa da Ingilishi.

Sai Moses Gyang mai lakabin Boss, mai shekararsa 25, fari ne dogo, ya bar gashi mai yawa a kansa, sannan ba ya da zane a fuska. Yana da aure kuma yana da sanko, dan kabilar Berom ne da jin harshen Hausa da Ingilishi.

Rundunar ta bukaci jama’a su taimaka don kai rahoto ofishinta mafi kusa idan an ga wadanda ake nema ruwa-a-jallon, ko a kira lambobi kamar haka: 08038907662 da 07059473022 da 09053872296 ko kuma 08075391844.