✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Galadima Nasir da kansa ya ce ni zan gaje shi – Galadima Saddiq Mahuta

A gobe Asabar za a yi bikin naxin tsohon Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Saddiq Abdullahi Mahuta a matsayin Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi na…

A gobe Asabar za a yi bikin naxin tsohon Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Saddiq Abdullahi Mahuta a matsayin Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi na 11 a fadar mai martaba Sarkin Katsina (Dokta) Abdulmumini Kabir Usman. Aminiya ta samu tattaunawa da sabon Galadiman, wanda ya bayyana cewa marigayi Galadima na 10, Mai Shari’a Mamman Nasir ya tava furta cewa shi zai gaje shi a wannan sarauta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Allah cikin ikonSa kai ne ka kasance na 11 a matsayin Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi. Yallavai, lokacin da aka ambata ka a wannan sarauta, yaya ka ji a ranka?

To, alhamdu lillahi. Shi irin wannan al’amari, al’ada ce ta xan Adam ya yi murna, sai dai kuma ba a daxewa ana murna sai mutum ya fara tunanin irin nauyin da Allah Ya xora masa. Don haka muke ta addu’a ga Allah Ya yi mana jajagora, domin ba qaramin al’amari ba ne, ka zo a damqa maka jagorancin al’umma.

A Musulunci, shi shugaba na al’umma, to duk wani haqqi na al’ummar nan yana kansa. Ya tabbatar da cewa ya yi masu adalci, ya taimake su, ya kare su daga wasu abubuwan da ba su iya kare kansu. To, ka ga ba qaramin al’amari ba ne ba. Muna cikin wani yanayi mai wahala qwarai da gaske, abubuwa sun yi tsauri ga al’umma, ga talauci, ga jahilci, ga abubuwa nan marasa kyau da ake aikatawa – da sace-sacen mutane da sace-sacen dukiyoyinsu, ga varna, a kwashe shanunsu, ga su nan dai iri-iri. To wannan mawuyacin hali ne. Na shigo cikin wannan al’amari a cikin wannan hali, to in ban da Allah da kuma abin da ni na sani, zan yi qoqari daidai gwargwado, domin babu mai iya yi mani shugabanci cikin wannan al’amari sai Allah.

Ina neman fahimtar jama’a, domin akwai abubuwan da za mu iya yi, akwai waxanda za mu sa hukuma ta wajen gwamnati ta qaramar hukuma ko ta jiha, su dubi wannan al’amari wanda ya taso, ko wanda zai taso.

Wannan sarauta ta Galadima, xaya ce daga manyan masarautu a Masarautar Katsina, idan muka koma baya, ko za mu iya samun tarihinta a taqaice?

Alhamdu lillahi. Wannan masarauta ta kafu tun kafin zuwan Turawa, lokacin da Shehu Usman Xanfodiyo ya yi Jihadi. Sarkin Katsina na wancan lokacin, kamar yadda tarihi ya gaya mana, Umarun Dallaje ya je ya amso tuta wajen Shehu Mujaddadi. To akwai su kakannin-kakanninmu, Fulani ne kuma malamai ne. A wani fanni na tarihin an ce su ma sun nufi Sakkwato domin su amso tutar sarautar Katsina amma sai aka ce shi Umarun Dallaje ya riga su zuwa. Duk da cewa ya riga su zuwa, ashe kuma shi Shehu ya riga ya samu labarin waxannan Fulani, kakanninmu. Don haka sai ya ce wa Umarun Dallaje ya je wuri kaza, can Paapu, wajen qasar Matazu, idan ya je zai iske waxannan Fulanin. Mutanen kirki ne masu arziki kuma masu ilimi ne. Y ace masa ya yi tafiyar mulki tare da su.

To ilai kuwa haka ya faru, domin kuwa Umarun Dallaje yana dawowa zai wuce Katsina da tuta, ya zo ya samu waxannan Fulani ya ce masu to ga saqo daga Shehu Usman Xanfodiyo. Nan take kuwa suka bi, suka yi mubayi’a ga sarki, aka taho Katsina. Haka aka ci gaba da tafiya har aka kai ga kafa gundumomi a masarutar Katsina. A kan haka aka ba kakannin-kakannin namu sarautar Galadima, amma suna zaune a cikin birnin Katsina. Abin da ya kama tun daga Damari zuwa dukkan Kudancin Katsina, duk mulkin Galadima ne. A taqaice wannan shi ne xan bayani game da asalin wannan sarauta ta Galadiman Katsina.

To ko mene ne matsayin wannan sarauta ta Galadima a masarautar Katsina?

Matsayinta shi ne, ita sarauta ce ta Hakiman Karaga, waxanda suka kasance guda huxu ne, wato da Qaura da ’Yanxaka da Galadima da kuma Durvi – su ne idan babu sarki, za su duba su ga cikin masu haqqi na gado, wanda ya fi cancanta ya zama sarki, sai su zartar.

Ganin girman wannan sarauta ta Galadima kuma da ganin cewa gidajen da ke da haqqi suna da yawa, ko za ka yi mana bayanin yadda takara ta kasance a wannan sarauta bayan rasuwar Galadima na 10, marigayi Mai Shari’a Mamman Nasir?

To, kamar yadda ka ce, duk wani xan Galadanci vangaren maza, wanda yake ’ya’yan maza, to yana da haqqi ya nemi Sarautar Galadima. Lokacin da wannan sarauta ta zo, bayan rasuwar shi Mai Shari’a Mamman Nasir, aka zo aka yi zaman ta’aziyya, na tara wasu daga cikin ’ya’yansa tare da Danejin Katsina, na gaya masu cewa zan fito neman sarauta; domin bai kamata mu voye wa juna ba, cikinku ban san wanda zai fito ba. To amma kowane ne ya fito, duk wanda ya samu, ko ba a cikinmu nan da muke nema ba, in dai xan Galadanci ne, to haqqinmu ne mu ba shi goyon baya, mu yi masa mubaya’a kuma a ci gaba da zumunci. To a haka muka rabu amma sauran waxanda suka shiga takara, ban yi magana da su ba amma dai na samu labarin cewa kamar mutum bakwai ne suka nemi sarautar kuma muka yi takara da su. Allah dai Ya qaddara ni ne na samu wannan sarauta. To ina qara godiya ga Allah kuma ina neman taimakonSa a kan tafiyar da al’amuran wannan sarauta.

Akwai xan uwanka, wato yayanka Dokta Tukur Abdullahi, wanda tun can ma da farko shi aka yi tsammanin zai zama Galadiman Katsina na goma amma Allah bai yi ba. To ko a wannan karon ya nemi takarar ko kuwa yaya abin yake?

Shi tun Galadima Nasiru ma yana da rai, ya ce ko sarauta ta faxi ba ya sha’awa, domin abin da yake gani, girma ya kama shi. To kuma akwai wata xabi’a ta shi marigayi Mamman Nasir, duk inda muka je, zai nuna ni ya ce ga fa wanda zai gaje ni nan. An sani ana raha ne amma ban san abin da ke cikin zuciyarsa ba. Amma domin a yi raha, yana ce wa dangi, yanzu fa sarautar Galadima ta zamanto sai wanda ya yi shari’a.

Farko-farkon hawansa Galadima, mun je Katsina an yi rasuwa gidan sarki, lokacin Sarki Kabir Usman, sai ya ce mu je in raka shi da wasu sauran dangi. Muka je muka yi wa sarki ta’aziyya sai ya ce wa Sarki Kabir “Allah taimaki sarki, ko na mutu, ga wanda nake so ya gaje ni nan.” Shi ne har na maida Magana, na ce wa sarki ba da gaske yake ba. Haka dai aka yi wasa da dariya, domin shi mutum ne mai son raha qwarai da gaske.

To ranka ya daxe Galadima, ko yaya dangantakarku take da shi marigayi Galadima na 10, Mamman Nasir?

Wato dangantakarmu da shi marigayi abu ne mai ban mamaki qwarai, musamman ga mutane da yawa da ba su sani ba. Da mahaifinsa, Kogo Abdullahi da mahaifinmu. ’yan uwa ne. Shi Kogo Abdullahi mahaifin Galadima Nasir, xan Galadima Abu ne. Shi kuma mahaifinmu, xan Xanranko Sani ne. To da Xanranko Sani da Galadima Abu da Xangaladima Abdullahi, uwarsu xaya, ubansu xaya. To ka ga ai kusancin ya kai kusanci. To kuma ban da wannan, da mahaifiyata da mahaifiyar Mamman Nasir, babansu xaya. To ka ga ta kowane vangare xan uwana ne.

Wani al’amari kuma tsakaninku da marigayi Mamman Nasir shi ne, shi ya kasance a vangaren Shari’a, haka kai ma abin da ka yi ke nan. Shin ko akwai wata shawara tsakaninku yadda kuka kasance a cikin wannan aiki haka?

Gaskiya wannan qaddara ce ta Allah kawai, domin ni ban tava gaya masa cewa ina son in yi Shari’a ba. Kuma tun da farko ma ina makaranta, ban tava qudurta cewa zan yi Shari’a ba amma da na koma makaranta a shekarar 1971, na je Kwalejin Bayero (Jami’a), a lokacin nan tana liqe da Jami’ar Ahmadu Bello. A nan na yi karatun share fagen shiga jami’a (Preliminary Studies). Abin da na maida hankali a lokacin shi ne Nazarin Harshen Ingilishi, lokacin kusan mu uku ne a ajin, waxanda babu kamar mu a wannan fannin. A lokacin nan, kasancewar Kano na da zafi sosai, sai in kama rashin lafiya, wasu quraje suna fito mani a jiki. Don haka shi malaminmu, wanda Bature ne, mukan zauna mu yi hira. Sai na shaida masa cewa ni ba ni iya zama a Kano saboda haka zan koma Zariya in karanta fannin Shari’a. Ni kuma haka nan na faxi haka, shi kuma ya ce bai yarda ba. shi ne duk na gaya masa dalilaina na rashin lafiya. Dayake suna da fahimta, sai ya ce lallai ina da hujja, ya ce zai ma taimaka mani koda an samu matsala wajen neman gurbi. A haka na baro Kano na dawo Zariya na fara karatun Shari’a kuma lokacin ma Mamman Nasir bai ma san an yi haka ba.

Yallavai ko yaya dangantaka take tsakaninka da Sarkin Katsina na yanzu, Abdulmumini Kabir Usman?

Sarki na yanzu, mai martaba Dokta Abdulmumini Kabir Usman, mun saba da shi qwarai da gaske tun yana Magajin Gari, kai tun ma yana makaranta, domin muna gabansu a makaranta. Shi ya yi karatu a Jami’ar Usman Xanfodiyo Sakkwato, ni kuma na yi Jami’ar Ahmadu Bello Zariya amma mukan xan haxu haka idan wani abu ya tashi. To da na dawo Katsina da aiki, yana matsayin Magajin Gari sai muka qara qulla zumunci qwarai, muna gaisawa. A kai-a kai nakan je gidansa, idan muna neman wani abu na taimakon al’umma game da abubuwan da ke faruwa game da Ma’aikatar Shari’a, nakan je in neme shi shawara. Haka shi ma idan ya ga akwai wasu abubuwan da ake yi, ka san shi da yake kullum suna samun koke daga wurin mutane, yakan nuna mana ga koken mutane dangane da abubuwan da ake yi a Ma’aikatar Shari’a. To wannan ya qara sa muka shaqu da shi sosai, domin shi ya yi suna tun yana Magajin Gari. Ba ya da kwaxai, domin wani lokaci sai ya tashi bai da ko kwabo, wallahi. To haka sai ta’adarmu ta zo xaya da shi, muna ta zumunci har Allah Ya sa akwai wata qanwarmu da ta yi aure a Kano, suka rabu da mijin ta dawo nan Katsina wurina, har ya gan ta ya ce yana so. Ya zo aka yi magana aka ba shi. Wannan ya qara danqon zumuncina da shi, ta kai ga har bayan da ya zama sarki, akwai abubuwa na shawarwari, waxanda in na ga ya kamata in ba shi; sai in je in same shi, daga ni sai shi sai Allah, in ce masa mu ga yadda muke ganin al’amura. Wasu ya amsa, wasu kuma ya yi mani bayani idan akwai buqata. To waxannan abubuwan su ne suka qara sa muka qara qulla danqon zumunci tsakanina da shi qwarai da gaske.

Yallavai Galadima, daga qarshe ko akwai wani bayani na qashin kanka da ban tambaye ka ba, da kake son al’umma su sani?

Qwarai da gaske akwai amma bari in ba ka shi a taqaice. Abin da muke so mu nuna wa jama’a, babu yadda za a yi jama’a ta tafi ba tare da shuwagabanni ba. Saboda haka shi shugaba, shi ne zuciyar al’umma. Idan shugaba ya lalace, to al’umma ta lalace, kamar yadda Manzon Allah (saw) ya ce, idan zuciya ta lalace to duk jiki ya lalace. To abin da nake son gaya wa jama’a a vangarenmu, idan Allah Ya so kuma Ya yarda, za mu ba da shugabanci nagari, za mu yi wa kowa adalci. Su kuma suna da haqqin mu ma su yi mana adalci da biyayya da shawarwari nagari waxanda idan aka haxa qarfi da qarfe, muna fatan Ubangiji zai tsirar da mu daga cikin mawuyacin halin da ake ciki.