Search
Subscribe
Galadima Tijjani Hashim: Rumfar fadar Kano ta fadi

Galadima Tijjani Hashim: Rumfar fadar Kano ta fadi

Da safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba  ne Allah Ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim rasuwa a Abuja kuma a wannan ranar  aka yi jana’izarsa a birnin Kano, inda aka binne shi a makabartar dandolo da ke yankin Gwauron Dutse, da misalin karfe uku da minti 22 na ranar.
dimbin jama’a ne suka halarci jana’izar  marigayin a kofar Kudu ta fadar Kano, wacce Limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen ya jagoranta da misalin karfe biyu da minti 53. Manyan mutanen da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Namadi Sambo da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da kuma mukaddashinsa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da  Alhaji Lawal Kaita da Alhaji Isiyaka Rabi’u da Sarkin Ringim, Alhaji Sayyadi Mahmud Ringim da tsohon Hafsan mayakan sama, Nura Alkali da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da sauran fitattun mutane na cikin Kano da waje ne suka halarci jana’izar.
Marigayi Tijjani Hashim ya rasu yana da shekara 79, kuma yana daga cikin kadan daga cikin tsofaffin manyan hakiman fadar Kano da suka yi saura. Kuma shi mutum ne mai karfin fada-a-ji, ba a fadar Kano kadai ba, har ma da jihar Kano da Najeriya gaba daya, saboda  kasancewarsa tsohon ma’aikacin gwamnati da ya yi aiki a karkashin marigayi Firimiyan Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato.
Haka nan mukamin Galadima shi ne mafi girma a fadar Kano, kafin daga bisani, marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya maida Wamban Kano shi ne mafi girma a jerin hakiman fadar Kano. Duk da haka Galadima yana daya daga cikin manyan hakimai biyar ko shida da suke nada sarki a fadar Kano.
Matsayin da marigayin yake da shi da kuma alfarmar da yake da ita ga dimbin manyan mutane a fadin Najeriya ya sa mutane da yawa suna zuwa wajensa neman alfarma da kamun kafa don neman aiki ko makaranta ko wata alfarmar daban, daga waurare daban daban, kuma galibi suna dacewa da hakan.
Alhaji Lawal Kaita da d an majalisa Faruk Lawal sun bayyana shi da cewa mutum ne wanda kodayaushe kofarsa a bude take wajen taimakon jama’a da nemar musu alfarma. Haka ma mutane da dama da Aminiya ta ji ta bakinsu, sun bayyana shi da cewa an yi rashin mutumin da yake taimakon jama’a, musamman wajen samun aiki a gwamnatin tarayya.
daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Aminu Tijjani Hashim, ya bayyan cewa ba gaskiya ba ne da ake cewa Galadima ya rasu ne a asibitin Abuja, kuma ya je Abuja ne daga nan zai wuce kasar waje neman magani. Ya ce mahaifinsu ya je Abuja ne kamar yadda ya saba zuwa lokaci lokaci kuma ya bar gida cikin koshin lafiya da nufin zai dawo Kano ranar Litinin.
Ya ce, “mun girgiza kwarai da jin labarin rasuwarsa a safiyar ranar da yake shirin dawowa Kano, domin ni dai na yi masa gani na karshe ne a ranar Alhamis, kuma ban ga wata alama wani da ke alamta cewa zai rasu ba.”
daya daga fadawan marigayi Galadima, Injiniya Abba Abubakar ya shaida wa Aminiya cewa, sun kai har karfe daya da minti 6 suna hira a daren da ya rasu, kuma suna raha suna dariya. Ya ce “har muka rabu bai nuna alamun zai rasu ba, sai dai ya yawaita cewa gobe da safe karfe 10 za mu bar Abuja mu kama hanyar komawa Kano.” Ya ce sun dade suna hira da shi da Mansur Isa Bayero da Ibrahim karaye, kuma dakunansu suna kusa da na Galadima a masaukin nasu.
Ya kara da cewa, da misalin karfe hudun dare da majidadin Galadima, Abdulkadir Akawal ya je zai tashe  shi ne, don ya ce a tashe shi zai yi nafila kuma zai dauki azumi, sai ya tarar ya rasu. Daga nan suka buga wa tsohon Likitan sarki da ke Abuja, Mista Oseidu, wanda ya zo aka kai gawar asibitin Abuja, aka tabbatar ya rasu.
An haifi marigayi Galadiman Kano a shekarar 1935, iyayensa su ne marigayi Hashim Abbas da Hajiya Binta. Ya yi firamare ta Bebeji a shekarar 1944, sannan ya shiga makarantar Midil ta Kano a 1948, sannan an nada shi dan Isan Kano da kuma Kansilan harkokin Al’umma da ci gaba, a shekarar 1966. A shekarar 1976 ya zama cikakken dan majalisa masarautar Kano. Ya zama Turakin Kano a shekarar 1989, sannan ya zama Galadima a 1992.
Bayan sarauta, marigayi Galadima dan kasuwa ne da yake da kamfanoni da kamfanin Jirgin sama na Trans Air da yakan yi jigilar alhazai a duk shekara, sai dai ikon Allah a wannan shekarar kamfaninsa bai samu shiga jigilar alhazai ba.
Manyan mutane daga wurare daban daban sun ci gaba da zuwa ta’aziyyarsa, da suka hada da tsohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar da Muhammad Sani Abacha da Walin Katagum, Ambasada Adamu Aliyu da Gwamnan jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko da sauransu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin