Search
Subscribe
Game da kara haraji

Game da kara haraji

A cikin ’yan kwanakin nan muka ji cewa Majalisar Dokoki ta Kasa ta tabbatar da sabuwar Dokar Kudi wacce  za ta kara harajin kaya da yin haka zai iya jawo hauhawar farashin kayan masarufi. Allah Ya jikan Umaru Musa ’Yar’aduwa domin wannan haraji da ake maganarsa an ce shi da ya zo rage shi ya yi. Haka zalika man fetir a bisa al’ada shugabanninmu kara kudinsa suke amma shi ragewa ya yi. Irin wadannan matakai da ’Yar’aduwa ya dauka tabbas ba karamin saukaka rayuwar talaka suka yi ba, kuma ya yi ne duk don talakan ya san ana yi da shi.

Shi ya sa a kullum nake fadin kaf shugabannin Najeriya da na ga mulkinsu Umaru Musa ’Yar’aduwa ne, na yi amanna ya zo da salon mulkin da talaka zai ji dadi kwana kusa.

Allah Ya jikansa, Ya sa can ta fi nan, Malam Umaru Musa ’Yar’aduwa. In da wani hakkina a kanka na yafe maka duniya da Lahira. Talakawan Nijeria na jin jiki, muna addu’ar Allah Ya kawo mana mafita.

Nasiru Kainuwa Hadeja 08100229688

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin