✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganawa da Hafsat Suleiman: Makauniyar da ta zama lauya

Masu iya magana sun ce nakasa ba kasawa ba, wannan ya fito fili kan dagewar da Hafsat Suleiman haifaffiyar garin Kaduna, wadda ta makance tun…

Masu iya magana sun ce nakasa ba kasawa ba, wannan ya fito fili kan dagewar da Hafsat Suleiman haifaffiyar garin Kaduna, wadda ta makance tun tana karama kuma a kwanan nan ta kammala digirinta na lauya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma ta samu kwarewa a  aikin lauya. Jama’a da dama sun taya Hafsat murnar wannan nasara a shafukan sada zumunta. A  hira ta musamman da Aminiya, Hafsat ta bayyana gwagwarmayar da ta sha kamar haka:

 

Garin yaya kika rasa ganinki?

Ina karamar yarinya lokacin, ba zan iya tunawa ba koda kuwa an ba ni labari.

Wadanne irin kalubale kika fuskanta wurin neman ilimi a kokarinki na zama lauya?

Da farko dai na rasa damar zaben makarantar da raina ke so kamar kowane mutum, ala tilas na shiga makarantar koyar da nakasassu ta Jihar Kaduna saboda ita ce makarantar da mutane irina ke iya halarta. Bayan na kammala firamare na shiga Kwalejin ’Yan Mata (WTC) ta Katsina, daga bisani na shiga makarantar ’yan mata ta Girls High School a Jos, inda na yi aji 1 da aji 2 na karamar sakandare. Daga nan na koma Abuja, inda na kammala karatun sakandare a Sakandaren Gwamnati da ke Kwali. Bayan haka ne na shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya don karatun lauya.

A jami’a kam kalubalen ya fara ne tun daga farko, inda Shugaban Sashen ya ce ba za su dauke ni ba saboda babu kayan aikin da za a yi amfani da su wurin koyar da ni. Cikin taimakon Allah da kuma kokarin wadansu mutane ya yarda aka dauke ni. Sauran kalubale sun hada da sayen littattafan karatu saboda babu allon rubutu irin namu. Tilas sai na nemi wani domin ya karanta mini ko kuma in biya a rubuta mini a kwamfuta ta yadda ita kuma za ta karanta mini.

Wadansu daga cikin malamai sun taimaka mini kwarai da kwafin kwamfuta na littattafan da muka nazarta a aji, wadanda su ne dama suka wallafa su, amma idan na tambayi wadansu cewa suke ba su da shi, wadansu kuma ko kallona ma ba sa yi. Amma cikin taimakon Ubangiji na yi nasara.

Ta yaya kike zirga-zirga a cikin makaranar?

Na samu mutane masu kirki sosai da suka taimaka mini, wadansu ma ba ’yan ajinmu ba ne amma haka za su yi mini jagora zuwa aji. Hatta lokutan da kawayena ba sa kusa, ina samun mai taimakawa, sukan ajiye abin da suke yi su raka ni masaukina.

Me ya sa kika yanke shawarar yin karatun lauya?

Ban taba tunanin zama lauya ba ko a lokacin da nake karama saboda mahaifina ya fi son in zama mai gashin kashi da kuma kula da marasa lafiya (physiotherapist), kuma har zuwa lokacin da na gama sakandare haka na kudurce a raina. Amma daga baya da na fuskanci cewa yanayin ba mai sauki ba ne sai na yanke shawarar canja kwas amma duk da haka ban yi tunanin aikin lauya ba. Hakazalika ban taba sha’awar karanta kwas din da aka kebance ba domin masu lalura ta musamman saboda har kullum ba na son al’umma ta rika yi mini kallon marar amfani saboda nakasar da nake da ita.

A lokacin da ina makarantar sakandare, wani mai aikin bayar da shawara ya gaya min cewa ba zan iya karanta kimiyya ba saboda haka dole sai dai in zabi bangaren adabi ko kuma zamantakewa. Na dade ina tunanin abin da zan karanta a bangaren adabin sai daga baya dai na yanke shawarar karatun lauya saboda ina da sha’awar taimaka wa marasa karfi wurin neman ’yancinsu.

Wane kira za ki yi ga masu lalura ta musamman?

Ina kiransu da kada su gajiya, su yi gwagwarmaya don cimma burikansu.

Mene ne kudurinki na gaba, tunda yanzu kin zama kwararriyar lauya?

A yanzu haka ina aiki da wani kamfani na lauyoyi kuma ina fatan in zama cikakkiyar lauya bayan hidimar kasa (NYSC), sai dai matsalar al’umma na da karancin fahimta game da mu. Na sani cewa abu ne mai wuya a dauke ni domin kare wani mutum a kotu saboda lalurata, kuma ko da na samu aikin idan tsautsayi ya sa aka yi rashin nasara mutumin zai dora laifin a kan cewa saboda ina da lalura ce. Ya kamata al’umma su daina nuna mana wariya.

A lokacin da nake halartar makarantar masu bukata ta musamman na lura cewa ana tilasta wa kananan yara su zauna tare da manya domin daukar darasi, wanda hakan bai da ce ba domin yana shafar fahimtarsu. Ina addu’ar Allah Ya ba ni dama domin in kafa gidauniya ta musamman wadda za ta tallafa wa yara masu bukata ta musamman, kuma zan yi alfahari ko da kuwa yaro daya ne ko biyu na taimaka mawa.