✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje da zababbu daga Kano sun karbi satifiket din nasararsu a zabe

A shekaranjiya Laraba ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta raba takardun shaidar cin zabe ga mutanen da aka zaba a mukamai…

A shekaranjiya Laraba ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta raba takardun shaidar cin zabe ga mutanen da aka zaba a mukamai daban-daban da suka fito daga Jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen taron bayar da satifiket din Shugaban Hukumar INEC a Jihar Kano Farfesa Riskuwa A. Shehu ya ce dukan mutanen da aka ba takardar shaidar, hukumar ta tabbatar da cewa sun cika ka’idojin da ta shimfida musamman samun kuri’u mafiya rinjaye a kan abokan takararsu.

Farfesa Riskuwa ya ce mulki mai inganci yana tabbata ne kawai idan har masu mulki suka ji tsoron Allah.

Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje tare da Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna sun karbi nasu satifiket din a daidai lokaicn da sauran zababbun da suka samu nasarar samun kujeru uku a Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakila 24 da kuma wadanda aka zaba a Majalisar Dokokin Jihar duk sun karbi satifiket dinsu.

Aminiya ta lura cewa ’yay’an Jam’iyyar PDP wadanda suka samu nasarar cin zaben kujeru 12 daga kujerun Majalisar Dokokin Jihar 40 ba su halarci taron ba.

Jam’iyyar PDP ta bayyana dalilinta na kaurace wa taron bayar da satifiket din inda ta ce ba ta amince da wurin da aka tanada domin gudanar da taron ba ne wato rufaffen dakin taro na Sani Abacha da ke Kofar Mata inda ta ce mambobinta ba su da cikakkiyar kariya a wannan wuri.

A cikin wata takarda da Kakakin dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, ya ce Jam’iyyar PDP ta bayyana matsayarta tun a farko, inda ta rubuta wa Hukumar INEC takarda tana neman a canja wurin gudanar da taron wanda zai zama na kowa da kowa amma ba mallakin gwamnatin jihar ba. “PDP ta nemi Hukumar INEC ta canja wurin taron wanda zai zama na kowa da kowa kamar yadda aka yi a lokutan baya musamman a shekarar 2011 da shekarar 2015,” inji shi.

Jam’iyyar PDP ta ce hakan ne ya sa ta umarci mambobinta su kaurace wa halartar taron karbar satifiket din har sai Hukumar INEC ta saurari korafinta tare da biya mata bukatarsu. “Abin takaici ne yadda Hukumar INEC ta zama ’yar amshin shatan Gwamantin Jihar Kano da kuma Jam’iyyar APC,” inji shi.