✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje na neman diyyar bata suna Naira biliyan 3 daga Jaafar Jaafar

Gwamann Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shigar da karar kamfanin jaridar DAILY NIGERIAN tare da mawallafin jaridar Jaafar Jaafar, akan neman diyyar Naira biliyan 3…

Gwamann Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shigar da karar kamfanin jaridar DAILY NIGERIAN tare da mawallafin jaridar Jaafar Jaafar, akan neman diyyar Naira biliyan 3 saboda  laifin fallasa bidiyon da ke nuna cewa, Gwamnan na karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta fitar da rahoton cewa, babbar kotun jihar ne ta sanar da hakan wata daya kenan bayan fallasa bidiyon.

Lauyan Gwamnan Nuraddeen Ayagi, ya bukaci kotun da ta umarci mawallafin jaridar da ya biya diyyar bata suna na Naira biliyan uku.