✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya karbi Rabi’u Sulaiman Bichi a gidan gwamnati

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga mabiya Kwankwasiyya da su hada hannu da gwamnati domin ciyar da jihar gaba. Ganduja ya…

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga mabiya Kwankwasiyya da su hada hannu da gwamnati domin ciyar da jihar gaba.

Ganduja ya yi kiran ne a daren ranar Laraba bayan ya karbi tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Kano wato Rabi’u Sualiman Bichi, wanda ya sauka daga shugabancin jam’iyyar ta PDP kuma ya koma jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa Rabiu Bichi, ya isa gidan gwamnatin Kano tare da dumbin magoya bayan Kwankwasiyya da wasu daga cikin shugabanninta na kananan hukumomi, wadanda suka yi aiki a karkshin Rabiu Musa Kwankwaso lokacin yana gwamnan Kano.

Ganduje ya shawarci ‘yan Kwankwasiyya da su, “Koma gida domin yin aiki tare da gwamnati”. “Wadanda suka kai mu gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Koli sun yi abin da kundin tsarin mulki ya ba su dama ne. Saboda haka muke kiran ‘yan hamayya da su zo mu yi aiki tare domin ciyar da Kano gaba,” in ji Ganduje.

Shi kuwa shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas taya ‘yan Kwankwasiyyar murna ya yi kuma ya ce: “Yau ranar tarihi ce ta bikin binne PDP magoya bayan Kwankwasiyya a Kano biyo bayan ficewar wanda ya kafa ta.”

A jawabinsa yayin taron, Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana cewa ya koma jam’iyya mai mulki ne ta APC saboda kiran da Gwamna Ganduje ya yi wa ‘yan hamayya na yin aiki tare da gwamnati.

Rabiu Bichi, shi ne sakataren gwamnatin Ganduje a karon farko da APC ta lashe zabe a jihar kafin daga bisani dangantaka ta yi tsami tsakanin Ganduje da Rabi’u Musa Kwankwaso, abin da ya janyo ya sauka daga mukaminsa.