✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya rantsar da sabbin alkalai shida

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin alkalan Babbar Kotun Jihar guda shida da zumman rage jinkirin shari’o’i. Gwamnan ya ce karin…

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin alkalan Babbar Kotun Jihar guda shida da zumman rage jinkirin shari’o’i.

Gwamnan ya ce karin yawan alkalan zai kuma taimaka gaya wajen samun adalci da damar sauraron kowane bangare a kotunan jihar.

Ya ce dukkannin sabbin alkalan da aka rantsar sun cancanta, domin sun ci jarabawa tare da samu yabon Hukumar Kula da Alkalai (NJC).

Gwamnan wanda ya ce bangarori uku na gwamnati a jihar za su yi aiki tare domin amfanin jama’ar jihar, ya bukaci sabbin alkalan da su kare mutuncin da aka sansu da shi da na bangaren shari’a.

Antoni Janar na Jihar, Muhammad Lawa ya ba wa sabbin alkalan rantsuwar kama aki a ranar Juma’a.

Sabbin alkalan da suka karbni ranstuwar su ne:  Abubakar  Maiwada, Maryam Sabo, Zuwaira Yusuf A, Jamilu Sulaiman, Sunusi Ma’aji dsa kuma Hafsat Yayha Sani.‎

Gwamnan ya kuma rantsar da Alhaji Aminu Bahaushe‎ a matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatar Gidaje da Sufuri.