✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garabasar da ke tare da sayen Hannun Jari (2)

Na yi shimfidar wannan makala a makon da ya gabata, inda na yi bayani a kan garabasa kashi uku da dan kasuwa zai iya samu…

Na yi shimfidar wannan makala a makon da ya gabata, inda na yi bayani a kan garabasa kashi uku da dan kasuwa zai iya samu idan ya sayi hannun jari. Garabasar farko daga biyun da na yi bayani a kanta ita ce ta samun sukunin lura da habakar jarinsa, ko akasin haka a kowane mako, wato zai iya kiwon jarinsa tamkar akuya ko tinkiya. Akwai wadatattun bayanai a kullum a kafofin yada labarai game da kamfanonin da ke kasuwar hannun jari,wato wadanda jama’a suka sayi hannayen jarinsu. Wadannan bayanai za su ba dan kasuwa sukunin da zai iya kiyaye jarinsa yayin da zai iya lura da farashin kamfani ko kamfanonin da ya zuba jarinsa; wato zai iya janyewa daga kamfanin da ya ga babu alheri cikinsa ya mayar inda yake ganin ya fi alfanu. A nan ne na ja hankalin dan kasuwa a kan cewa wannan garabasa ce da ba a samun irin ta a sauran kafofi na kasuwanci kamar harkar kasa, wato saye da sayar da fulotai da gidaje da kuma sauran harkokin yau da kullum.
Garabasa ta biyu da na haska wa dan kasuwa a makon jiyan ita ce, ta damar  da dan kasuwa zai samu na cin riba daga kamfanonin da kwararru ke tafiyar da su inda ake samun ingantacciyar riba da ke wanzuwa a dalilin kwarewar wadannan ma’aikata da kamfanin ya dauka. A nan na yi tsokaci cewa idan ba ta hanyar sayen hannun jari ba, dan kasuwa mai karamin jari ba zai iya tsara kamfani ba har zai iya daukar ma’aikata kwararru irin haka ba masu basira ba har ya amfana daga basirarsu ba. Na ce da kudi kalilan dan kasuwa zai iya sayen jarin kamfaonnin man fetur ko na masana’antu ko na bankuna, da sauran irin wadannan manyan kamfanoni masu albarka.
Garabasa ta uku da na yi wa dan kasuwa albishir da samunta idan ya sayi hannun jari  ita ce ta samun shawarwari da kulawar  kwararru tun daga ranar farko da ya yi wannan yunkuri, har ya zuwa ranar da ya daina wannan harka a rayuwarsa. dan kasuwa zai samu irin wadannan shawarwari daga wakilansa na saye da sayar da hannayen jari a farashi kalilan. Wadannan shawarwarin ne za su ba dan kasuwa samun riba mai tsoka, su kuma kare shi daga munmunar asara.
Garabasa ta hudu kuma wacce zan dora a yau, ita ce ta sukunin mayar da kadara tsaba, ko kuma musayar haja. Kasuwar hannun jari a bude take a kullum, daga Litinin zuwa Juma’a, saboda haka a duk lokacin da dan kasuwa ya bukaci ya sayar da hannun jarinsa sai kawai ya tuntubi wakilinsa da nufin sayarwa, inda zai karbi kudinsa a cikin wadansu sa’o’i kalilan. Haka kuma idan ya so kara yawan hannayen jarinsa ko a kamfanin da yake da hannayen jari ko a wani, maganar wadansu sa’o’i ne in dai har yana da kudin a kasa. Hakazalika, dan kasuwa na iya musayar hannayen jarinsa a kowane lokaci, misali ya sayar da wadanda ke hannunsa ya sayi na wadansu kamfanonin da ya fi so.
Garabasa ta biyar ita ce ta inganta garke. dan kasuwa kan samu karin hannayen jari daga kamfanonin da ya sayi hannayen jari a matsayin garabasa, wato abin da ake ce wa, ‘bonus shares’ da Turanci. Wannan garabasa na samuwa ne a karshen shekara bayan kamfanoni sun yi lissafi sun raba ribar da aka samu ga masu hannun jarin kamfanonin sai kuma a raba hannayen jari na garabasa, inda za a iya cewa an ba kowane mai rike da hannun jarin kamfani hannun jari daya ga kowadanne hannayen jari biyu da yake da su. Wato idan dan kasuwa na da hannun jari 200 a wannan kamfani, zai samu karin hannun jari 100 ke nan, ya kasance yana da hannayen jarin kamfanin 300 ke nan.