✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane: Galadiman Katsina ya tsallake rijiya da baya

A ranar Litinin da ta gabata da misalina ƙarfe 9:00 na dare ne wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane suka kai wa Galadiman…

A ranar Litinin da ta gabata da misalina ƙarfe 9:00 na dare ne wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane suka kai wa Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Mai shari’a Mamman Nasir hari a kan hanyarsa ta komawa gida. Mutanen sun kai hari ne a tsakanin kauyen Gora zuwa ’Yarmama a hanyar zuwa Malumfashi, inda suka rutsa da Galadiman da Shamakinsa mai suna Aminu sai kuma direban motarsa mai suna Abdurrahman. Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da Aminu, yayin da Galadiman da direbansa suka tsira, bayan samun dauki daga ’yan sanda cikin lokaci kamar yadda Kakakin Rundunar DSP Gambo Isa ya ce.

Aminiya ta tantubi wadansu a garin Malumfashi inda suka ce, da ma wannan wuri ana fama da matsalar fashi da makami.

Sarkin Fulanin Galadiman Alhaji Aminu ya ce an kai wa Galadiman harin da ake da yakinin masu garkuwa da mutane ne suka kai shi, domin sun tafi da shi yaron da ke gaban motar Galadiman yayin da ake kokarin kawo musu dauki.

Alhaji Kabir Sakaina wani mazaunin garin Malumfashi ya ce, Hakimin yana nan gidansa a halin yanzu cikin koshin lafiya babu wani abin da ya same shi.

Sai dai har zuwa rubuta wannan rahoto babu wani bayani game da rahotonnin da ke yawo a kafafen sadarwar zamani cewa, maharan sun tafi da jakar da ake kyautata zaton ta Hakimin ce da ake cewa akwai kudi a ciki tare kuma da karbe musu wayoyi. Kuma babu wani bayani daga masu garkuwar kan halin da Aminu da suka tafi da shi yake ciki.

A wani labarin, masu garkuwa da mutanen sun sace Mai unguwar garin Zandam mai suna Babangida Lawal da wani ɗan kasuwa. An ce maharan sun shiga garin Zandam da ke Karamar Hukumar Jibiya cikin dare ranar Lahadin da ta gabata inda suka je gidajen mutanen suks fito da su bayan balle kofofin gidajensu.

Wata majiya ta ce lokacin da maharan ke yunkurin tafiya da Mai unguwar jama’a sun fito kai dauki inda wadansu suka samu raunuka.

Kazalika, maharan sun yi awon gaba da wasu shanu a garin Gurbin Magarya da ke Karamar Hukumar Jibiya.

Babu wani bayani daga masu garkuwa da mutanen kan neman biyan kudin fansa.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin Kakakinta DSP Gambo Isa inda ta kara da cewa suna bincike a kan lamarin.