Da Dumi Dumi

Garkuwan Chindo ya sake zama Sarkin Damben Gargajiya

Sarkin Dambe Garkuwan Chindo da koriyar alkyabba
Sarkin Dambe Garkuwan Chindo da koriyar alkyabba

Garkuwan Chindo zai ci gaba da zama Sarkin Damben Gargajiya karo biyu a jere, bayan da ya yi nasara a kan Abdurrazak Ebola. Tun a 13 ga Oktoba  Garkuwan Chindo da Guramada da Ebola da Bakude suka tashi dambe babu kisa a wasan da suka yi a gidan dambe da ke Dandalin Ado Bayero da ke  Kano.

Wani rahoto da Sashin Hausa na BBC ya wallafa a shafinsa na Intanet ya bayyana cewa, wannan ne karo na biyu a jere da Garkuwan Chindo ya yi nasara a kan Ebola a wasan karshe, inda a bara a filin wasa na Kano Pillars ya lashe kyautar motar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan sarautar ana kiranta da sunan Muhammdu Sunusi II, inda Masarautar Kano kan bayar da doki da kayayyakin nadin sarauta da sauran kyautukan alfarma. Ita kuwa Kungiyar Dambe ta Jihar Kano takan bayar da mota ga wanda ya zamo zakara da babur na hawa ga wanda ya yi na biyu da kuma kudi ga wanda ya yi na uku.

Bahagon Shagon ’Yan sanda yana daga cikin ’yan damben da suka kara a gasar bana, amma aka cire shi, sakamakon bai samu halartar fili ba a lokacin da zai yi wasa. Bahagon Shagon ’Yan sanda shi ne ya lashe motar damben Katsina da aka yi, bayan da ya yi nasara a kan Dogon Aleka a wasan karshe.

Garkuwan Chindo ya kai wasan karshe ne, bayan da ya doke Ali Kanin Bello, shi kuwa Ebola nasara ya yi a kan Bahagon Sanin Kurna. Yanzu dai ya rage wasan karshe na Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da za a yi nan gaba.

ADVERTISEMENT

Cikin wadanda suka rage sun hada da Dogo Mai Takwasa da Dogon Kyallu dukkansu daga Guramada sai Ali Kanin Bello da Bahagon Shagon ’Yan sanda su kuma daga Arewa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya