Search
Subscribe
Gasar Firimiya:  Gobe Arsenal za ta kece raini da Liberpool

Gasar Firimiya: Gobe Arsenal za ta kece raini da Liberpool

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Arsenal da na Liberpool a gasar firimiyar Ingila.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasan Arsenal da ake kira Emirate.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake matsayi na biyu a teburin gasar da maki 26 a wasanni 10 yayin da Arsenal yake matsayi na 4 da maki 22 a wasanni 10.

Kenan, wasan na gobe zai yi matukar zafi, don dukkan kungiyoyin biyu suna neman nasara ne don ganin an dama da su a kokarin lashe gasar ta bana.

Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil da masoya kwallon kafa don ganin yadda wasan zai kaya.

Fatar mu dai a yi kallon wasa lafiya, kuma a tashi lafiya.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin