✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Gobe Chelsea za ta kece raini da Liberpool

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Chelsea da na Liberpool a gasar firimiyar Ingila. …

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Chelsea da na Liberpool a gasar firimiyar Ingila.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 5 da rabi na yamma agogon Najeriya a filin wasan Chelsea da ake kira Stamford Bridge.

Liberpool ce take saman tebur da maki 18 bayan ta yi nasara a dukkanin wasanni 6 da ta yi yayin da kulob din Manchester City yake matsayi na biyu da maki 16 a wasanni 6.  Sai kulob din Chelsea a matsayi na uku da maki 16 a wasanni 6 yayin da kulob din Watford yake matsayi na hudu da maki 13.

Kenan,  za a kara wasan gobe ne a tsakanin Chelsea da take matsayi na uku da Liberpool da ke jan ragamar gasar.

Idan Chelsea ta samu nasara to za ta karya lagon Liberpool kenan amma idan Liberpool ta samu nasara a kan Chelsea, za ta ci gaba da rike kambunta a matsayin ta farko.

Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil da masoya kwallon kafa don ganin yadda wasan zai kaya.