✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya:  Gobe za a yi gumurzu tsakanin Arsenal da Chelsea

A gobe Asabar ce ake sa ran za a fafata  wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila, inda kulob din Arsenal zai hadu da…

A gobe Asabar ce ake sa ran za a fafata  wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila, inda kulob din Arsenal zai hadu da Chelsea a wasan da ake yi wa lakabi da Gumurzun Landan.  Wasan zai gudana ne a filin wasa na Arsenal wato Emirate da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.

Dukan kungiyoyin biyu suna zaune ne a birnin Landan da hakan ya sa ake yi wa wasan lakabi da “Karon Battar Birnin Landan.”

Kawo yanzu kulob din Chelsea ne yake matsayi na 4 a teburin gasar yayin da Arsenal ke matsayi na biyar.  Duk wanda ya yi sake aka doke shi, to na iya fuskantar matsala, ganin yadda gasar ta dauki zafi.

A wasan zagayen farko kulob din Chelsea ya lallasa na Arsenal da ci 2-1 don haka a wannan karo kulob din Arsenal zai yi kokarin fanshe cin da aka yi masa.

Idan kulob din Arsenal ya yi sake aka doke shi ko ya yi kunnen doki, sannan Manchester United ta samu nasara a wasanta da Brighton, United ce za ta koma ta biyar a teburin gasar yayin da Arsenal za ta koma ta shida.

Magoya bayan kulob din Arsenal dai sun nuna rashin gamsuwa ganin yadda suka taba ba kulob din United tazarar maki 8 amma a halin yanzu suka hada maki daidai, sai  bambancin yawan kwallaye kawai.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya.