Search
Subscribe
Gasar Firimiya: Jibi za a kece-raini a tsakanin Chelsea da Liberpool

Gasar Firimiya: Jibi za a kece-raini a tsakanin Chelsea da Liberpool

A ci gaba da fafatawa a Gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ne kulob din Chelsea zai kece-raini da na Liberpool a wasan karo na 6.

Wasan zai gudana ne a filin wasan Chelsea na Stamford Bridge da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake matsayi na farko a gasar bayan an yi wasanni biyar da maki 15 ba tare da yin kunnen doki ko rashin nasara ba, yayin da Chelsea ke matsayi na 5 bayan ya hada maki 8 a wasanni biyar.

Wasan na jibi zai yi zafi, don Chelsea za ta yi kokarin doke Liberpool ne don ta taka mata birki yayin da Liberpool kuma za ta yi kokarin ci gaba da nuna kwazo don kada a karya mata lago.

Sai dai kafin wasan, kulob din Leicester City zai hadu da na Tottenham yayin da Manchester City zai hadu da Wattford a gobe Asabar.

Sai a jibi Lahadi da misalin karfe 2:00 na rana agogon Najeriya kulob din West Ham zai kece-raini da Manchester United.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin