✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar zakarun kulob-kulob na Turai: Madrid ta yi wa Galatasaray luguden kwallaye

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya yi raga-raga da kulob din Galatasaray da ke Turkiyya da…

Gareth Bale da Cristiano Ronaldo a lokacin da suke murnar yi wa kulob din Galatasaray luguden kwallaye a ranar Talatar da ta wuceA ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya yi raga-raga da kulob din Galatasaray da ke Turkiyya da ci 6-1 a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
Wasan ya gudana ne a Turkiyya a gaban magoya bayan kulob din Galatasaray da suke hankoron kunyata Real Madrid a wasan farko.
Sai dai dan kwallon tsakiya a kulob din Madrid mai suna Isco ne ya fara zura kwallon farko ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.  Bayan da aka dawo ne dan kwallon gaba a kulob din Madrid Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye uku yayin da takwaransa Kareem Benzema ya jefa kwallaye biyu.  Ana gab da tashi wasan ne sai dan kwallon Galatasaray mai suna Umut Bulut ya jefa kwallo daya a ragar Madrid da hakan ta sa aka tashi wasan da ci 6-1.
Kocin Galatasaray mai suna Fatih Terem ya bayyana bacin ransa ganin yadda kulob din Madrid ya bi su har gida ya yi musu luguden kwallaye da hakan ta sa tilas su zage damtse a sauran wasannin da suka rage don hayewa zagayen wasa na gaba.