✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Zakarun Turai:  Kocin Barcelona ya ji dadi rashin haduwa da Liverpool a zagaye na biyu

A ranar Talatar da ta wuce ce jaridar Mole Sport ta kalato yadda kocin FC Barcelona na Sifen Ernesto Balberde ya rika yin murna ganin kulob…

A ranar Talatar da ta wuce ce jaridar Mole Sport ta kalato yadda kocin FC Barcelona na Sifen Ernesto Balberde ya rika yin murna ganin kulob dinsa ba zai hadu da na Liberpool da ke Ingila a zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai ba, bayan fitar da jadawalin gasar da Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta yi.

Hukumar UEFA ta fitar da jadawalin kulob 16 da suka kai wannan mataki na wasannin zagaye na biyu, inda  FC Barcelona  za ta hadu da kulob din Lyon na Faransa yayin da Liberpool za ta kece raini da kulob din Bayern Munich da ke Jamus.

“Mara tunani da wayo ne kadai zai yarda ya hadu da kulob din Liberpool a wannan lokaci”, inji Balberde.

Sai dai masana harkar kwallo suna ganin kocin yana yin shagube ne kawai, don FC Barcelona tana takama da zaratan ’yan kwallon da suka fi na Liberpool irin su Lionel Messi da Luiz Suarez da Dembele.

Ana sa ran a watan Fabrairun 2019 ne za a ci gaba da zagaye na biyu na gasar daga nan ne za a tantance kulob 8 da za su haye matakin kwata-fainal.

Kawo yanzu kulob din Liberpool bai samu rashin nasara ba a gasar rukunin Firimiya na Ingila, al’amarin da ya sa yake saman teburin gasar.