Search
Subscribe
Ghana za ta biya Najeriya gininta da aka rusa a Accra

Sashen ofishin jakadancin Najeriya da ‘yan bindiga suka rusa a Ghana

Ghana za ta biya Najeriya gininta da aka rusa a Accra

Gwamnatin Ghana za ta biya Najeriya ginin ofishin jakadancinta da aka rusa a birnin Accra na kasar ta Ghana.

Kakakin Malisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce takwaransa na Ghana Aaron Mike Oquaye, ya tabbatar masa ta wayar tarho cewa majalisar da bangaren zartarwar kasarsu za su gana domin sasanta matsalar a diflomasiyyance.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun rusa sabbin gine-ginen masaukan da ake yi a ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar Ghana.

Lanre Lasisi, Mai magana da yawun Gbajabiamila ya ambato mai gidan nasa na cewa Mista Oquaye ya ce gwamnatin Ghana za ta mallaka wa Najeriya sabon ginin da dukkan takardunsa, sannan an kamo tare da fara bincikar wadanda suka rusa ginin a baya.

A ranar 24 ga watan Yuni ne Gbajabiamila ya ce zai gana da takwaransa na Ghana, domin abin da aka yi a ofishin jakadancin cin fuska ne ga Najeriya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin