✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidan talabijin na farko a Afirka ya yi bikin cika shekara 60

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bukukuwan murnar cika shekara 60 da kafa gidan talabijin na farko a Afirka wato Gidan Talabijin na Jihar…

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar da bukukuwan murnar cika shekara 60 da kafa gidan talabijin na farko a Afirka wato Gidan Talabijin na Jihar Yamma ta Najeriya, (WNTB) wanda tsohuwar Gwamnatin Jihar Yamma a karkashin jagorancin marigayi Cif Obafemi Awolowo, ta gina a 1959 a Ibadan. An gudanar da bikin ne a karkashin shugabancin tsohon ma’aikacin gidan talabijin din  Ambasada Yemi Faounbi wanda ya taba zama Shugaban Hukumar Gudanarwar gidan.

Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Rauf Olaniyan ne ya wakilci Gwamna Seyi Makinde a wajen fara bikin da aka gudanar a harabar Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ke Agodi a birnin Ibadan.

Bikin ya kara samun armashi ne a dalilin halartar tsofaffin ma’aikata maza da mata da suka yi aiki a sassa daban-daban na WNTB da gidan rediyon Jihar Yamma (WNBS) da  mafi yawansu suka kai shekara 80 zuwa sama.

An gabatar da wadansu daga cikinsu ga Mataimakin Gwamnan inda ya ce labarinsu kawai yake ji bai sansu ba, sai yanzu da ya yi ido biyu da su. Shugaban Kwamitin Bikin Ambasada Yemi Farounbi, ya jagoranci ayarin Mataimakin Gwamnan da manyan mutane da suka halarci bikin zuwa dakin da aka baje kolin hotunan tsohon Firimiyan Jihar Yamma marigayi Cif Obafemi Awolowo da tsohon Ministan Kudi Cif Anthony Enahoro da marigayi Cif T. T. Solaru, wadanda suka yi fafutikar tabbatar da samun gidan talabijin din a wancan zamani wanda shi ne talabijin na farko a Najeriya da Afrika baki daya da aka gina a Ibadan hedkwatar tsohuwar Jihar Yamma mai kunshe da jihohi 6 a yanzu.

Hotunan da aka baje kolinsu, sun hada da na tsofaffin ma’aikata da suka hada da matar da ta fara karanta labarai cikin harshen Yarbanci.

Daraktan shiyya na NTA Ibadan, Injiniya Omolola Olorode, ita ce ta karanta jawabin maraba ga mahalarta bikin, yayin da Cif Sanya Oyinsan da Cif Adio Akingbogun suka yi jawabai a madadin tsofaffin ma’aikata.

Aminiya ta samu jin ta bakin wata tsohuwar ma’aikaciya mai suna Mama Bola Alo, wacce ta fara aiki da WNTB a 1960 inda ta ce “Godiya ga Allah ya kamata in yi saboda har yanzu ina nan da rai da koshin lafiya. Mun fara aiki tare da Turawa ne da suke koya mana abubuwa daban-daban a wancan zamani ba kamar yanzu da al’amura suka canja ba. Kuma aikin jarida ya fi muhimmanci a wancan lokaci fiye da yanzu da komai za ka ji maganar kudi kawai ake yi sabanin wancan lokaci da aka sa aikin a gaba fiye da kudi.”