Search
Subscribe
Gidauniyar ci gaban garin Gaidam ta bai wa Marayu 82 kayan sallah

Marayun da suka samu tallafin kayan Sallah a Gaidam

Gidauniyar ci gaban garin Gaidam ta bai wa Marayu 82 kayan sallah

Gidauniyar ci gaban garin Gaidam,  ta “Gaidam Community Association Foundation” dake jihar Yobe ta raba wa Marayu 82 kayan sallah dan su ma su samu sabon kaya kamar masu iyaye.

Da yake zantawa da Aminiya Jim kadan bayan sun raba kayan a garin Gaidam, Shugaban kungiyar Tijjani Maikeli, yace sun zabo  Marayun a tsakanin al’umma saboda akwai su da yawa a tsakanin yan Uwa da suke bukatar a taimaka musu.

Yace cikin Marayu 82 da suka bai wa kayan sallar, hudu daga cikin ‘yan wani kauye ne kusa da Gaidam mai suna Palgeri, da suma aka basu tallafin.

Tijjani Maikeli, ya kara da cewa kungiyar tasu karama ce saboda wannan shi ne karo na biyu da suka bada tallafi wa Marayu. Sai dai kafin nan suna gudanar da aikin gayya na gyaran kwalbatoci da sharar makabarta da sharar cikin gari lokaci zuwa lokaci.

Yace su da kansu ne ke tattara kudaden a tsakanin su hada, idan shekara tayi sai su zauna su ga yadda za su bada tallafin.

Tijjani Maikeli, ya kuma ce abunda suka so bayar wa sun so yafi haka amma saboda wasu daga cikin su ‘yan kasuwa ne ba su samu damar bayar da gudumawar su ba saboda kasuwarsu ta Gaidam ta kai wata hudu a rufe ba a  komai.

A cewar sa sun taba  bai wa marayun tallafi na kayayyakin karatu musamman littatafai da kayan karatu dan rage musu radadi.

Sannan kuma nan gaba za mu yi shiri na musamman dan fadada wannan shiri kuma za muyi shi da wuri. Inji Maikeli.

Wasu daga cikin Marayun da suka samu tallafin sun godewa kungiyar ci gaban garin Geidam bisa tallafin da suka basu na sababbin kayan sallah kamar kowa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin