✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Daily Trust ta horar da ’yan jarida a Abuja

A farkon makon nan ne Gidauniyar Daily Trust tare da hadin gwiwar Gidauniyar MacAuthur ta fara horar da ’yan jarida sanin makamar aiki a kan…

A farkon makon nan ne Gidauniyar Daily Trust tare da hadin gwiwar Gidauniyar MacAuthur ta fara horar da ’yan jarida sanin makamar aiki a kan binciken labaran kwa-kwaf ta hanyar bidiyo da sadarwar zamani.

Taron horarwar wanda akalla ’yan jarida 38 daga kafofin watsa labarai daban-daban suka halarta, ya gudana ne tun daga ranakun Litinin zuwa jiya Alhamis a otel din Links da ke yankin Utako, Abuja.

Da yake jawabi a wajen bude horon, Shugaban Gidauniyar Daily Trust, Alhaji Wada Maida ya ce horar da ’yan jarida yana cikin ayyukan inganta kwazo da rayuwa da Kamfaninn Daily Trust ke yi, inda ya hada tallafin da kamfanin ke ba ’yan gudun hijira da tallafa wa dalibai mata masu karatun kiwon lafiya da sauransu a matsayin sauran ayyukan gidauniyar.

A cewarsa, ’yan jarida na bukatar irin wannan horo musamman a irin wannan lokaci da komai yake komawa ta Intanet. “Idan za mu fadi gaskiya, yanzu labaran da ake isarwa ta bidiyo ko Intanet sun fi saurin isar da sako. Misali, bidiyon Sanata Elisha Abbo wanda ake zarga da bugun wata mata mai jego. Ba domin bidiyon ya fito an gani ba, da watakila ba wanda zai san abin da ya faru. Amma da yake an ga bidiyon, sai nan da nan ’yan sanda suka fara bincike a kan lamarin. Majalisar Dattawa ma ta kafa kwamitin bincike. Shin za ka iya hada tasirin wannan bidiyon da labarin da aka buga a jarida?” Shugaban ya tambaya.

Malam Wada ya yaba wa Gidauniyar MacArthur bisa tallafin da take ba gidauniyar tasu.