✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara a kasuwanni: Ina mafita?

Kalmar Gobara tana nufin masifa ko wani iftila’i da kan afka wa dukiya ko kadarar al’umma kai wani lokacin ma da rayuwaka. An fi danganta…

Kalmar Gobara tana nufin masifa ko wani iftila’i da kan afka wa dukiya ko kadarar al’umma kai wani lokacin ma da rayuwaka. An fi danganta Gobara da varnar wuta, wacce kan tashi a Gidaje da Makarantu da Kasuwanni da Ma’aikatu. Gobara kan faru a matakai daban-daban. Idan za a tuna a lokutan baya gobara ta tashi a ma’aikatar ilimi ta tarayya, haka ma a Jihar Kano gobara ta tashi a makarantun kwana na Qwa da Dala da Jogana da Kwankwaso da Gwale da Gwarzo da Bichi da Dawakin Kudu da kuma Bagauda.
A vangaren kasuwanni za mu ga cewa ta afku a kasuwannin Kwari da Kurmi da Singa da kuma na kwanan nan kasuwar Sabon gari, duk dacewa ba wannan ne karo na farko da hakan kefaruwa ba.
A kowace shekara a wannan qasa ta mu ta Najeriya akan samu afkuwar wannan iftila’i na gobara a sassa daban-daban na kasuwanni, ta yadda hakan yake jawo asarar dukiyoyi masu ximbin yawa, ta yadda a sanadiyyar hakan manyan ‘yan kasuwa da ma qanana ke talaucewa watau karayar arziqi, sakamakon rashin kyakykyawan agaji daga mahukunta. Wani abin da zai ba wa al’umma mamaki shi ne sai ka ga wasu kasuwannin duk shekara sai sun ci wuta,  kai watama sai ka ga ta kanci wuta kamar kimanin sau uku ko fin haka a shekara. Misalin kasuwar Sabon gari da kasuwar Birnin Sakkwato. Wannan ne ya ja hankalin mahukunta da marubuta, kai har ma da sauran al’umma akan musabbabin wannan gobara ‘yar-yayi ko baqon al’amari a Arewacin qasar nan, ganin cewa mafi yawan wutar tana tashi  ne a talatainin dare.
A ranar Laraba 18 ga watan Faburairu na shekarar 2016 wani iftila’in gobara ya afku a kasuwar Singa a jihar Kano. Wutar ta fara ci ne daga misalin qarfe huxu na asuba, inda ta jawo asarar kimanin dukiya har kimanin Naira biliyan biyar.
A daren wata ranar Talata 17 ga watan Faburairu, 2016 gobara ta tashi a kasuwar Kurmi ta Jihar Kano misalin qarfe takwas na dare, inda gobarar ta jawo asara har ta kimanin naira Miliyan uku, duk da cewa a wannan kasuwa ba shi ne farau ba.
A ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2015 da ta gabata ne wata gobara ta tashi a kasuwar Sabon garin kano a vangaren ‘yan katako, inda wutar ta fara ci wajen misalin qarfe bakwai na yammacin ranar, a qalla kimanin rumfuna sama hamsin ne suka qone, inda hakan ya jawo asarar miliyoyin kuxi.
Haka kuma a daren ranar Jum’ar nan 25 ga Maris, 2016 wata gobarar ta qara afkuwa a kasuwar ta Sabon garin Kano, inda wutar ta tashi wajen misalin qarfe sha biyu na dare har yanzu wunin ranar Lahadi da vurvushin wutar, al’amarin da ya tada hankulan al’umma saboda ganin cewa a iya tarihi ba a tava samuun iftila’i irin wannan ba wanda ya xaga hankulan ilahirin al’ummar Najeriya – domin kuwa ba a ce iya Kano ba don ba su, kaxai abin ya shafa ba, ganin yadda qasashe da dama a Afirka ke mu’amalantar kasuwar.