Da Dumi Dumi

Gobara ta kashe jarirai 11 a asibiti a Aljeriya

Akalla jarirai 11 ne suka mutu yayin da gobara ta tashi da jijjifin safiyar ranar Talata a wani asibiti a kasar Aljeriya.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Kyaftain Nassim Bernaoui, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa an ceto mata 107 daga gobarar.

Kyaftin Bernaoui ya kuma ce an ceto wadansu ma’aikatan asibitin su 30.

“Sai dai mun yi bakin cikin rasa jarirai 11 wadanda wadansunsu suka mutu sakamakon konewa da suka yi wadansu kuma saboda hayakin da suka shaka,” inji shi.

Ba wannan ne karo na farko da aka yi gobara a bangaren haihuwa na asibitin Bachir Bennacer ba.

ADVERTISEMENT

Ko a watan Mayun bara, an yi gobara a sashin amma ba a samu asarar rayuka ba, inji Kamfanin AFP.

Share