✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone gidaje da kayan abinci a Jigawa

An samu tashin gobara da ta kone gidaje  a kauyen Barebari da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta…

An samu tashin gobara da ta kone gidaje  a kauyen Barebari da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) Alhaji Sani Yusuf ne ya tabbatar da hakan.

Alhaji Sani ya ce, hukumar SEMA zata magance dalilin aukuwar tashin gobarar wanda ta fara tun daga karfe 11 na safe zuwa karfe 6 na yamma a jiya Talata.

Sakataren ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN yau a Dutse babban birnin jihar cewa, gobarar ta kusa kone kauyen baki daya.