✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lamushe dukiya a kasuwar Singa

A karshen makon da ya gabata ne wata gobara ta tashi a kasuwar Singa da ke Kano, inda ta lamushe dinbin dukiya.Shugaban kasuwar  Alhaji Abdul’aziz…

A karshen makon da ya gabata ne wata gobara ta tashi a kasuwar Singa da ke Kano, inda ta lamushe dinbin dukiya.
Shugaban kasuwar  Alhaji Abdul’aziz dalha Musa ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta tashi tun misalin karfe 12 na dare har aka wayi gari tana ci. “ Gobarar wacce ba a san dalilin faruwarta ba, ta tashi ne da misalin karfe12 na dare, inda kuma har aka wayi gari tana ci. A gaskiya an samu asara mai dimbin yawa sakamakon wanann gobara.” Inji shi.
Wani wanda abin ya shafa mai suna Abdullahi Mohammd Sani da ke sayar da kayan abinci, ya bayyana cewa gobarar ta lashe kusan dukkanin kayayyakin da ke shagonsa, sai dai ya yi fatan gwamnati za ta kawo masa dauki don ya samu ya ci gaba da kasuwancinsa.
Shugaban ya yaba wa namijin kokarin jami’an kwana-kwana, inda suka tsaya tsayin daka har sai da suka ga wutar ta mutu.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnati a madadin ‘yan kasuwa da ta taimaka wa ‘yan kasuwan, musamman ma wadanda abin ya shafa. “ Muna kira ga gwamnati da ta duba abin da ya faru ta tallafa wa ‘yan uwanmu wadanda wannan bala’i ya abka musu.” Inji shi.