Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gobarar tankar mai ta kashe mutum 10 a Gombe

Rahotanni daga jihar Gombe na bayyana cewa, akalla mutum 10 suka mutu lokacin da wata tankar mai ta kama da wuta a yau Asabar, wasu motocin shiga suma sun kama da wuta.

Wanji ganau ya bayyanawa majiyarmu cewa, tankar  man ta hadu da wata babbar mota ce da ta dauko ruwan gora a hanyar ta na zuwa kudancin Gombe.

ADVERTISEMENT

A yanzu haka jami’an hukumar kashe gobara na jihar Gombe na ci gaba aikin kashe wutar.

ADVERTISEMENT