✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar kwallon dawaki a Katsina

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ne ake sa rn fara gudanar da gasar kwallon dawaki da aka fi sani da Polo karo na…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ne ake sa rn fara gudanar da gasar kwallon dawaki da aka fi sani da Polo karo na 90  tun daga lokacin da Sarkin Katsina Dikko ya kawo wasan bayan zuwansa kasar Ingila a 1921.
Wasan Polon nadaya daga cikin wasannin da ake alfahari da su a Jihar Katsina da ma kasa baki daya baya ga wasan kwallon kafa.
A gasar ta bana wadda kuma kamar yadda al’adar wasan take a duk shekara, akan bude gasar wasan ce  a Katsina wadda hakan ke bayar da dama ga sauran wuraren dake gudanar da wasan cigaba da a yankunansu.
Kafin Jihar Kano ta fita daga Hukumar shirra wasan Polo ta kasa watau NPLa can ne ake rufe gasar a duk shekara. Duk da ficewar Jihohin Kano da Oyo da Legas daga hukumar NPF hakan  bai hana shigowar manyan kungiyoyin wasan Polon iri nsu Ribicon da Mad Air da Profile ba.  Haka kuma akwai kungiyoyin da dama da suka fito daga Abuja da Kaduna da Zaria da Bauchi da Yola da Minna da Jos da kuma Fatakwal da suke da suke turo wakilansu  don shiga wannan gasar ta Katsina ba.
Kamar yadda Kyaftin din kungiyar Polon na Katsina Alhaji dahiru Bagiwa wadda ke karkashin shugabancin shugaban kungiyar na dindindin (Life Patron) kuma Tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita ya ce kungiyar ta yi kyakkyawan shiri don gudanar da wannan wasa cikin tsanaki inda ta dauki wasu matakai ciki har da na kayyade yawan tim biyu da suka fito daga kungiya ko gari daya akan shiga gasar cin kofi daya.
Kamar yadda kyaftin din ya shaida wa Aminiya, ita dai wannan gasa ana yin ta ne a garin Katsina don cin manyan kofuna da suka hada da kofin Najeriya wanda kuma shi ne babban kofi da kofin Janar Hassan Usman Katsina da kofin Talba da kuma kofin Kumasi.
Ya kara da cewa daga cikin wadanda za su fafata akan babban kofin akwai Ribicon na dan majalisa Hadi Sirika da na Kaduna Profile na Ibrahim Abba da kuma na Katsina Mad Air na Lawal dahiru Mangal.  A kofin Janar Hassan akwai Katsina Kangiwa da Yola Kombina da sauransu.
Dangane da batun masaukan ‘yan wasa da dawakansu, Manajan shirya gasar na kungiyar Majidadin Katsina Alhaji Abdu Usman ya ce,dama an san Katsina da batun karrama baki don haka sun tanaji duk wasu abubuwan da ake bukata don gudanar da wannan gasa ciki har da matakan tsaro.
Ana sa akalla kungiyoyi talatin ne za su fafata a gasar wacce za a kwashe kwana bakwai ana yi.