✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gonzalo Higuain ya sanya hannu a Napoli

Dambarwar canza sheka da dan wasan gaban Real Madrid yake neman yi za a iya cewa ta zo karshe, don a shekaranjiya Laraba ne kulob…

Gonzalo HiguainDambarwar canza sheka da dan wasan gaban Real Madrid yake neman yi za a iya cewa ta zo karshe, don a shekaranjiya Laraba ne kulob din Madrid da na Napoli suka kulla yarjejeniyar cinikin dan kwallon a tsakaninsu.
Rahoton da kafar sadarwar Goal.com ta kalato ya nuna tuni kulob din Napoli ya ajiye wa Madrid Yuro miliyan 37 sannan kulob din ya amince ya rika biyan Higuain albashin Yuro dubu 163 a duk mako. Kenan dan kwallon zai rika karbar zunzurutun albashin Yuro miliyan 42.3 a matsayin albashi kadai a duk shekara.
Kulob din Napoli ya ce, ya yi amfani da kudin da ya sayar da dan kwallon gabansa Edinson Cabani ne wajen cefano Higuain daga Real.
A watan jiya ne dai kulob din Arsenal da ke Ingila ya yi yunkurin dauke Higuain amma  ciniki a tsakanin kungiyoyin kwallon kafar biyu bai kaya ba, al’amarin da ya sa kulob din Real ya fasa sayar da dan wasan.  Amma yanzu da kulob din Napoli ya kara kudi a kan cinikin dan kwallon ta sa ciniki ya kaya a tsakaninsu.
Ana sa ran nan da makon gobe ne dan kwallon zai koma Italiya don cigaba da buga kwallo a karkashin koci Rafa Benitez.