✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Goodluck Jonathan sha wahalar maza

Gaskiyar lamari na yi nazari sosai kuma daga karshe na samu mafita wajen gane wai shin wane ne Goodluck Ebele Azikwe Jonathan? Da farko dai…

Gaskiyar lamari na yi nazari sosai kuma daga karshe na samu mafita wajen gane wai shin wane ne Goodluck Ebele Azikwe Jonathan? Da farko dai an ce malamin makaranta ne wanda Dokta ne kuma cikakken lakcara, sannan daga baya ya shiga siyasa ya zama ko dai shugaban karamar hukuma ko mataimaki, shi ne kuma sunan nasa na Mainasara wato Goodluck, sai kawai aka ji ya zama Mataimakin Gwamna wanda ana cikin haka Shugaba Obasanjo ya samu takaddama da Alamesiya, wato Gwamnan Bayelsa na da, ya sa aka tsige shi sannan aka mayar da Goodluck ya zama Gwamnan Bayelsa. Tabdijan, ka ji fa rabo cikin ruwan sanyi.

Ashe dai Obasanjo wato Shugaban Kasa daga 1999 – 2007, ya dade yana cutar da siyasar Najeriya duk da a nan Arewa ma musamman ta yamma ya sha yin wannan alkaba’i na dora gwamnoni bisa ga jama’a da karfin tuwo. Obasanjo bai bar Goodluck Jonathan haka ba, yana Gwamnan Bayelsa a 2007; lokacin barinsa mulki sai da ya kakaba wa ’yan Najeriya ababen assha; domin shi ne ya ce lallai sai marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya zama Shugaban Kasa, bisa zargi ya yi haka ne domin shi marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya zame masa saniyar tatsa, da abin ya kasance ba yadda ya so ba duk da ya dauko Goodluck Jonathan ya sa aka ba shi Mataimakin Shugaban Kasa don ya nuna wa kananan kabilun Najeriya su ma ana yi da su.

Haka dai abubuwa suka tafi har aka samu zaben da aka yi aka ce Shugaba Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa Allah Ya jikansa ya ci zabe.

To bayan ya sha jinya kuma Allah Ya dauki ransa sai aka ce Mainasara shi ne Shugaban Kasa tunda shi ne Mataimaki wanda haka ya faru kuma bayan ya gama wa’adi daga 2010-2011 aka yi zabe tsakanin Goodluck da Janar Buhari wanda hukumar zabe a karkashin jagoranta Farfesa Attahiru Muhammad Jega ta ce Ebele Azikwe Goodluck Jonathan ne ya ci zaben.

Ebele Jonathan cinsa ke da wuya kafin 2013-2015, sai PDP ta kwabe, wasu rikice-rikice suka auka musu tun daga korar Shugaban Jam’iyyar Alhaji Bamanga Tukur har wasu gwamnoni bakwai wadanda suka tsaya dole sai Shugaban ya sauka wanda hakan ya faru. Biyu ne kawai daga cikin gwamnonin bakwai suka kasance tare da jam’iyyar tasu wato, Alhaji Sule Lamido na Jigawa da Babangida Aliyu na Neja.

Gaskiya duk da cewa Janar Babangida ya yi uwa ya yi makarbiya ganin Jonathan ya yi mulki gaskiyar lamari an yi zaben 2015, kuma Jonathan yana kan mulki bai ci ba amma cikin lokaci kankane ya bada kai bori ya hau domin ya yi wa Shugaba Buhari fatar alheri domin kaunar zaman lafiyar Najeriya. Wannan karamci da ya nuna,ya tabbatar da cewa shi ba mutum ba ne mai zakewa bisa son zuciya.

Haka ko a kwana-kwanan nan ya ciri tuta domin zargin ko-oho da ake masa na zaben Bayelsa wanda har abokina Lamido ya yi masa zargi marar tushe ya manta cewa shi ma akwai zargi iri-iri a kansa da muka kasa barci a kansa domin soyayyar da shi bai ma san muna yi ba. Domin ba ma bukatar komai a wurinsa, abotarmu tun lokacin PRP ne wacce suka guje ta suka yi hannun riga da ita a wancan lokaci.

Ni, in ban da ana cewa Asiwaju yana bukatar zama Shugaban Kasar nan, nan gaba wato 2023, sai in ce don Allah mutane su dawo da Jonathan Ebele domin kaunar ’yan Arewa da yake yi tunda babu dalilin dawo da dan Arewa mulki a shekarar 2023. Tunda mu mun dana abar kuma ’yan Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu su dawo domin dora ayyukan kirki da Shugaba Buhari ya yi.

Ya zama wajibi ’yan Najeriya su ci gaba da addu’a domin zaman lafiyar Najeriya kuma shugabanni su ji tsoron Allah su dubi zaman don a samu zaman lafiya ko’ina a Najeriya, Allah Ya taimaka.

 

Kwamared Ibrahim Abdu Zango Kano, (08175472298)