✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudunmowar Musulmin farko ga harkar lafya

Mutane da dama sukan dauka tunda aikin likitanci na zamani daga Turawan Yamma ne, ba shi da wata alaka da addini ke nan saboda ba…

Zanen hoton masanin magunguna a Duniyar Musulunci, RazhiMutane da dama sukan dauka tunda aikin likitanci na zamani daga Turawan Yamma ne, ba shi da wata alaka da addini ke nan saboda ba su riki addini sosai ba. Sabanin haka a iya cewa gudunmowar manyan addinan duniya biyu tana daga cikin manyan abubuwan da suka gina harkar lafiya ta zamani.
Tun a zamanin da kunne ya girmi kaka, wato wajen shekaru kusan dubu goma da suka wuce, an san harkar magani a duniya, a kasashe irinsu Misra da Farisa da Sin da kuma Indiya. Amma magunguna ne na saiwoyi da ganyayyaki da ’yan dabaru a wancan lokacin. Daga bisani ne ilmin zamani ya bullo daga kasashen yamma.
Likitancin wannan zamani ya samo asali ne daga kasar Girka tun a shekarun 2000, kafin zuwan Annabi Isa (2000 BC), ta hannun wani mai suna Hippocrates, wanda bai da wani addini. Ya zauna a kan karan kansa ya karanci dan Adam ciki da bai, da ’yan magungunan da kowane sashen jiki ya fi bukata, ya rika rubutawa yana kuma koyar da tunanin nasa, daliban nasa ma suna kara tasu fahimtar. A haka ilmin sanin dan Adam ya bunkasa har ta zo sai da aka kafa jami’a babba a wannan kasa, ta koyar da aikin likita, wadda ta zamo cibiyar bidar ilmi daga ko’ina a Nahiyar Turai.
Yayin da Musulunci ya shiga kasashen yamma ta kasar Andalusiya (Spain) a shekarun 650 bayan zuwan Annabi Isa, ya tarar da irin wannan ilmi na likitanci amma bai rushe shi ba. Wasu daga cikin Musulmin wannan zamani sai suka dukufa suka shiga makarantun koyar da aikin likitanci suka koya, suka kuma kara nasu sanin da fahimta a kan wadancan na Turawan. Kuma har yau wasu daga cikin nasu karin na nan a cikin manhajar ilmin, ba a rushe su ba. Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin wadancan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne.
Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo:
Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD): Mutumin kasar Farisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu.   
Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da dari. Fitacce a cikinsu shi ne ‘Al-Hawi,’ wanda kundin bayanai ne a kan aikin likita da ya shafi magunguna da yadda suke aiki a jikinmu.
A wani shagube da ya taba yi wa wani mai maganin ciwon ido, wanda ya kawo masa magani don ya sa a idonsa, sai ya tambaye shi da ya yi masa bayanin yadda ido ke aiki amma ya kasa, don haka ya ce maganin karya ne. Wannan ne ke mana tuni da taka-tsan-tsan wajen sayen magunguna a wurin jahilai.
Ali Ibn Abbas: Haly Abbas (920-994 AD): Shi ma daga Farisa ya fito kuma ana ji da shi a duniyar likitanci. Ya ba da gudunmowa ta hanyar rubuta littattafai cikin harshen Larabci, wadanda suka fi bayani a kan bangaren kwakwalwa da cututtukanta da bayanan falsafar binciken kimiyya irin na zamani.
Abul kasim Al-Zahrawi: Abulcasis (936- 1013 AD): Wanda yake Balarabe ne wanda aka haifa a kasar Spaniya. Ya yi fice wajen zama likitan tiyata na farko na zamani a duniyar Musulunci saboda kirkiro kayan aiki na leka wurare da dama na jikin mutum da ya yi, fiye da dari biyu, wadanda daga su ne aka kera na wannan zamani. Shi ne kuma ya fara nuna wa duniya cewa za a iya samun juna biyu a wajen mahaifa saboda tiyatar da ya sha yi a wannan bangare.
Ya zama likitan Khalifan Musulunci a kasar Andalusiya, wato Khalifa Al-Hakam kuma ya rubuta littattafai da dama a kan aikin tiyata, wanda har yanzu akan samu manhajojin a littattafan wannan zamani. Domin karin bayani, za a iya bincikar Kitabut Tasrif.
Abu Ali Ibn Sina: Abicenna (980-1037): Shi ma mutumin kasar Farisa ne, wanda yake da baiwar kaifin hadda da tunani mai zurfi. Ya haddace Alkur’ani yana dan shekaru goma kacal, sa’annan ya zama likita yana dan shekara sha shida. Ya yi aikin duba marasa lafiya kyauta a wannan birni kuma ya zama babban likitan Khalifan garin.
Daga baya ya yi hijra ya nufi yamma, inda a hanya ya rubuta kundaye a kan bayanai na kula da lafiya da aikin likita, ya kuma koyar da dalibai. Wannan kundi wanda ake kira ‘kaanun fid dibb’ an dade ana amfani da shi a jami’o’in kasashen yamma na wancan lokaci, a matsayin littafin koyarwa.
Ga kuma irinsu Ishak Al-Ruhawi dan kasar Turkiya, wanda ya fara bayani a kan tarbiyyar likitoci; wato yin tsantseni da taka-tsan-tsan a kan aikin likita da hukuncin da ya kamata a ba likitoci masu ganganci da aiki a cikin littafinsa mai suna ‘Adab Al-Tabib.’ Shi ne kuma ya fara bayanin cewa kowane sabon abu aka samar a kimiyyar likita, dole a samu wasu kwararru a aikin su zurfafa bincike don tabbatar da sabon bayanin ko karyata shi.
Sai kuma wasu da dama irinsu malaman wadannan da muka lissafa wadanda ba su yi fice kamar dalibansu ba. Misali, malamin Al Razi, Abu Hassan Al-Tabari, wanda ya yi fice a harkar lafiyar yara.
Akwai kuma irinsu Abu Alhassan Ibn Al-Nafis, likitan kasar Suriya wadanda Turawa ma ba su sani ba ko kuma suka sani amma suka ki ambatonsu. Shi ne wanda ya fara bayanin yadda jini ke zagaya jikinmu, tun kafin ma a haifi Baturen nan William Harbey, wanda suka ce shi ya fara wannan bayani. Da dai sauran ire-irensu.

LAFIYAR MATA DA YARA

Ina neman karin bayani a kan tagwayen da ake haifarsu a manne da juna. Shin halitta ce haka ko dai wata matsala ce?
Daga Ali Fancy Garko
Amsa: Ba halitta ba ce, tangarda ko matsala ake samu yayin da dan tayin tagwaye ya zo rabewa a mahaifa. Irin wannan kan faru ne a ’yan tagwayen da suka fito daga dan tayi daya (tagwaye masu kama da juna). Ka san akwai kuma ’yan tagwayen da suke fitowa daga kwayaye daban-daban (tagwayen da ba sa kama da juna ke nan).
To idan dan tayin tagwayen ya zo rabewa, kamata ya yi a ce ya rabu gida biyu, kowane rabi ya zama jariri guda. To a irin wannan tagwayen da aike haifa manne da juna, dan tayin ba ya rabewa duka don haka sai su zama jarirai biyu a manne, ko wani sashe na jikinsu a manne da juna, gwargwadon dai yadda kwan ya ki rabewa.
Akwai sinadarin da aka alakanta rashinsa ga aukuwar irin wannan tangarda da ma sauran tangardar halittar jariri, irinsu yankakken lebe, kumburarren kai, cindo da dai sauransu. Wannan sinadari shi ne Folic acid, wani magani mai araha da ake ba duk mai juna biyu da ta je awo.
Akwai kuma sinadaran da aka alakanta shan su ga aukuwar irin wannan tangarda da ma sauran tangardar halitta. Wadannan sinadarai sun hada da wasu magungunan gargajiya da na Bature (shi ya sa a takardar bayanin kowane maganin nasara sai an rubuta baro-baro, ko a ba mai juna biyu ko kada a ba ta); da guba irinsu gubar dalma da sauransu.
A kimiyyance, babu hujjar da kan sa a ce mutanen boye ne ke sanadin aukuwar irin wannan tangarda.
A yi mini bayani game da kaciyar mata, domin an haifa mini ’ya mace matata ta dame ni da lallai na kai wa wanzami a yi mata kaciya. Ni kuma na ki yarda soboda na taba jin cewa wai tana da illa. To mene ne gaskiya?
Daga Adamu, Zariya
Amsa: Haka ne, a zahirin gaskiya kaciyar mata al’ada ce ta Larabawa wadda da addini ya zo bai rusa ba, sai dai ya ce a yi taka-tsan-tsan, amma karfin wannan bayani ma sai ka tuntubi malaman addini. A al’adar Bahaushe, ita aka fi sani da yankan gishiri, wadda an sha samu a wurin yankewar akan iya tabo jijiyoyin jini, jini ya tsinke ya yi ta zuba, a rasa jaririyar, ko a sa mata wata kwayar cuta a jikinta ta hanyar askar (kamar kwayar cutar kanjamau ko ta ciwon hanta) ko kuma a yanko mafitsara a sa mata ciwon yoyon fitsari, wadanda wadannan su ne illolin da kake ji ana fadi.
Sai mutum ya ga irin wahalar da matan kasashen Afirka Maso Gabas inda wannan al’ada ta fi kamari, wato kasashen Sudan da Ethiopia da Eritrea ke sha zai san ba kaciya kawai ake ba barna ake. A irin wannan kasashe inda ake wa mata fiye da rabi kaciya, fitsari ma wani gagararsu yake saboda girman barnar, balle zamantakewar aure. A likitance ana ganin cewa rashin yin ta ya fi yin ta zama lafiya, sabanin kaciyar maza.