✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudunmowar Naira Miliyan 50 na neman haddasa rigima tsakanin ’yan fim

Daga dukkan alamu dai, farfajiyar shirya fina-finai ta Najeriya na neman zama farfajiyar rigima a kan dukiya, domin kuwa a makon jiya ma wata rigimar…

Gwamna Akpabio yana mika cekin kudi ga Mista Zik Zulu Okafor, Shugaban kungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Najeriya, a UyoDaga dukkan alamu dai, farfajiyar shirya fina-finai ta Najeriya na neman zama farfajiyar rigima a kan dukiya, domin kuwa a makon jiya ma wata rigimar ta kunno kai, inda furodusoshi suka fara tada jijiyar wuya game da gudunmowar Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya ba su.
A watannin baya can, irin wannan rigima ta taba kaurewa tsakanin ’yan fim din, a lokacin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tallafa wa harkar fim din da bashin Naira biliyan uku. Kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu, har yanzu ba a gama warware wannan rigima ba, ga shi kuma sabuwa ta kunno kai.
A wannan karon kuwa, Gwamna Akpabio, alkawarin da ya dauka ne ya cika; kasancewar a watan Maris na bana ne ya yi alkawarin bayar da tallafi ga ’yan fim din.
Kamar yadda kafar watsa labaran ’yan fim a intanet, nigeriafilms.com ta ruwaito, Gwamnan ya mika cekin kudin ne ga hannun Shugaban kungiyar Furodusoshin Fim ta Najeriya, Mista Zik Zulu Okafor, a gidan Gwamnati na Uyo, wanda ya halarta tare da wasu daga cikin jiga-jigan kungiyar. Wadannan kuwa sun hada da Yakubu Abubakar (Sakataren kungiyar) da Andy Amenechi da Stephanie Okereke-Linus da sauransu.
Kamar yadda bincike ya tabbatar, an samu korafi daga wasu masu ruwa da tsaki a harkar ta fim, suna nuna tsoron cewa babu mamaki shugabanni a harkar za su murkushe tallafin. Sai dai a ta bakin Zik Zulu, wanda shi ya amshi cekin daga hannun gwamnan, ya musanta cewa akwai wani shiri na danne kudin.
“Wannan ne karo na farko da aka taba samun irin wannan gudunmowa mai tsoka, don haka abu ne mai yiwuwa mutane su rika nuna shakku ko korafi, amma ina tabbatar maka da cewa babu wanda zai taba ko kwabo. Za mu yi amfani da kudin nan ne wajen bunkasa harkar, kamar yadda aka bukata.” Inji Zik.