✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guragu sun yi wasan sada zumunta a ranar Sallah

A ranar Sallah karama da ta gabata ce kungiyar kwallon kafa ta guragu ta shirya wasan sada zumunta ga wadansu kungiyoyin kwallon kafa na guragu…

A ranar Sallah karama da ta gabata ce kungiyar kwallon kafa ta guragu ta shirya wasan sada zumunta ga wadansu kungiyoyin kwallon kafa na guragu da ke karkashinta.

Kungiyoyin da suka fafata a wasan su ne kungiyar kwallon kafa ta Guragu da ke Jihar Akwa Ibom da kuma takwararta ta Kalaba da ke Jihar Kuros Riba.

Wasan ya kayatar, ganin dukkan kungiyoyin biyu sun nuna bajinta da kuma kwerewa a yayin wasan.  Kuma an gudanar da wasan ne a filin wasa na Layin Mary Slessor da ke Kalaba.

Jama’a da dama ne ciki har da masu kafafu suka kalli yadda wasan ya kaya, kuma sun yaba matuka game da abin da suka gani.

Jama’ar da wakilinmu ya zanta da su jim kadan bayan an tashi wasan sun ja hankalin gwamnati da masu hannu da shuni  su rika tallafawa wasannin guragu (Para Soccer)  da hakan zai sa a rage yawan masu bara a titunan da ke fadin kasar nan.

Alhaji Mukhtari Abubakar Manga wani dan kasuwa da ke Kalaba ya bukaci gwamnati da masu hannu da shuni da ’yan majalisun tarayya da na jihohi da su yi wa Allah su rika tallafawa guragu wajen tafiyar da harkokin wasanninsu da hakan zai zage yawan barace-barace da suka yi.

Ya ce da yawa daga cikin guragun da ke zaune a Kudancin kasar nan sun baro iyalansu a gida (Arewa) da hakan ya sa suka bukatar tallafin da zai rika samar musu da kudin shiga don kula da iyalinsu.

Shugabannin da suka shiyra wasan sun ce sun yi haka ne don karfafa zumunci inda suka gayyato makwabta don nuna farin ciki musamman a ranar Sallah karama.