✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Buni ya jinjina wa Kamfanin Media Trust

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya jinjina wa Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya kan jajircewarsa wajen yada labaran…

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya jinjina wa Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya kan jajircewarsa wajen yada labaran abubuwan da suke faruwa a Jihar Yobe da Arewa maso Gabas baki daya, inda ya ce duk da kalubalen tsaro da ya addabi yankin, jaridun Trust suna kokari kullum wajen ba da sahihan rahotannin abubuwan da suke faruwa sannan kuma akan samu jaridun a wajen masu sayarwa a koyaushe.

Gwamna Buni ya bayyana haka ne  lokacin da ayarin shugabannin kamfanin a karkashin jagorancin Babban Jami’in Zartarwa kuma Babban Edita, Malam Mannir Dan Ali suka ziyarci Gwamnan a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Damaturu.

Wannan bayani yana dauke ne a wata takarda dauke da sa hannun Babban Daraktan Harkokin ’Yan jarida na Gwamnan, Abdullahi Bego, inda ya ce Gwamnan ya gode wa kamfanin kan yadda yake buga jaridar yara ’yan makaranta ta Teen Trust, inda ya  ce wannan jarida tana da matukar muhimmanci wajen karfafawa da fadada karatunsu da kuma kara musu himma da kwazo.

“Muna kokari mu dawo da matasa cikin hayyacinsu bayan gushewar Boko Haram, hakan kuma ba zai yiwu ba sai an ba su ingantaccen ilimi, don nan gaba su zama masu amfani a tsakanin al’umma da iyayensu da kasa baki daya,” inji shi.

Daga nan sai Gwamnan ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Yobe za ta rika sayen wannan jarida ta Teen Trust domin yara a rika ajiye ta a dakunan karatu na makarantu a duk fadin jihar.

Shugaban ayarin ya jinjina wa Gwamnan kan yadda Gwamnatin Jihar Yobe take bai wa Kamfanin Media Trust hadin kai da goyon baya.

Malam Mannir Dan Ali ya ce kamfanin yana shirin kaddamar da tashar talabijin mallakinsa nan gaba kadan domin sun samu lasisi daga Gwamnatin Tarayya, sai ya kara da cewa za su ci gaba da tafiyar da tsarin labaransu bisa ka’ida.