Da Dumi Dumi

Gwamna Gaidam ya hori sababbin shugabannin dananan hukumomi kan ridon amana

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya hori sababbanin shugabannin dananan hukumomin jihar 17 da aka zaba kan su ride amana kuma su nesanta kansu daga facaka da kudaden al’umma da za a ba su don gudanar da ayyukan raya dasa a yankunansu.
Alhaji Ibrahim Gaidam yayi wannan gargadi ne lokacin da yake rantsar da sababbin shugabannin a Damaturu, inda ya ce ya zama wajibi sababbin shugabannin dananan hukumomin su kula da amanonin da jama’a domin tsira a nan duniya da Lahira.
Ya shawarce su kan su jajirce wajen gudanar da ayyukansu kuma su bude dofofinsu ga jama’arsu don isar da koken-kokensu ba tare da samar da tazara tsakaninsu ba wadda hakan shi ne dimokuradiyya.
Ya ce zaben dananan hukumomin ya gudana cikin kwanciyar hankali, sabanin maganganun ’yan adawa da furucin Shugaban Hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega na rashin yanayi mai kyau da zai iya sa ba za a iya gudanar da zaben badi a jihar ba.   
 Gwamnan ya ce masu irin wannan furuci kamar Minista a Ma’aikatar Kudi Yerima Ngama suna yi ne kawai don sun san ba su da kowa a Yobe, don haka suke gudun in an yi zaben za su ji kunya, sun san Jam’iyyar APC za ta lashe zaben, kuma ga shi ’yar manuniya ta nuna APC ta lashe zaben da aka yi, za ta ci gaba da kare kambinta a jihar kiuma ta lashe zaben dasa baki daya domin PDP ta mutu murus.
A ranar Asabar da ta gabata ce Jam’iyyar APC ta lashe zaben dananan hukumomin 17 da kansiloli 178, a zaben da PDP ta daurace masa, yayin da wasu jam’iyyu 10 suka fafata.
A zagayawar da Aminiya ta yi lokacin zaben a dananan hukumomin Damaturu da Tarmuwa da Bursari ta ga yadda masu kada duri’a suka yi cincirindo a rumfunan zaben.
Sakatariyar dungiyar Hukumomin Zabe na Jihohi kuma Shugabar Hukumar Zaben Jihar Kaduna, Hannatu Binyad da ke cikin shugabannin hukumomin zabe na jihohi 11 da suka halarci zaben, ta ce ta sha mamaki yadda ta ga jama’a sun fito don kada duri’unsu ba tare da matsala ba, inda ta ce hakan ya nuna cewa za a iya gudanar da zabe a jihar ba tare da fargabar matsalar tsaro ba.

Share