✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna mai sunan sulalla

Gwamna mai sunan sulalla na Jihar Jijjiga-ciyawa jarumin jamj’iyya mai dan boto da sanda jirge ne, wanda ke yi mata yaki a daidai lokacin da…

Gwamna mai sunan sulalla na Jihar Jijjiga-ciyawa jarumin jamj’iyya mai dan boto da sanda jirge ne, wanda ke yi mata yaki a daidai lokacin da take durkushewa. Domin baya ga rungumo Rigima da ya yi don kakaba wa al’ummar jiharsa, a matsayin gwamna gwarangwam, ya ma himmatu ka’in da na’in wajen dura ashariya ga jiga-jigan jam’iyyar maganin sarawar kurungu. A makon da ya arce, an jiwo mai girma gwamna gwarangwam yana cacakar Malam Nasara El-Rusau da Gwamna Mai kwarankwatsin-tsiya na birnin Dabo, wai sun yi wa mai dan boto butulci.

Batu na ingarman karfen karafa, da Babangada-gada ne, kuma ya saba da irin wannan baranbaramar, da sai in ce sai an kula ba-haya yake wari, tunda shi da ma Gwamnan Jihar Ni-na-ja ya saba da mina-mina. Kenci dai ta iya kici-kici.
Shi kuwa mai sunan sulalla jira kawai yake yi talgen tuwo ya sulalla, don ya ji dadin sulalewa da sulalla, amma sai ya hango sanwar da aka dora ba za ta dahu ba. Domin samartakar kusu da lakume kudin lukudi ta zo karshe. Kifi na ya fasko jirginka mai jar koma. dauki dora! Ba ma yi!
’Yan makaranta, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido, da ke cikin Amintattar jaridar kasar Haurobiya, kusan cewa mun sha caccakar Malam Nasara El-Rusau, a zamanin da yake rike da mukamin Magajin garin babban birnin Haurobiya, watu Haurubja, amma daga bisani muka fasko cewa, Baba-ojo mai gonakin Ottawa shi ne ya ba shi izinin yin rusau, har ta kai ga muka dauka ya yi amfani da wani kundi mai taken “Matsala falan-falan: Cikakken ikon rusau.” Duk da cewa ayyukan da ya gudanar a Haurubja sun takura wa talakawa, yanzu ana ganin alfanunsu. Domin da bai gyara zaman masu kwararowa wannan birni ba, tabbbas da ya zama “Cunkus: dakin tsummokarai.” Bisa la’akari da dimbin basirar Malam Nasara el-Rusau, muna ganin tabbas shi al’ummar Jihar Bayan-Kada ya kamata su zabo, a matsayin gwamnansu. Domin aikata sabanin haka na iya haifar musu da zaben tumun dare. Ni dai ban ce komai ba game da Yaron Bayan-Kada, domin ban san wani aiki da ya yi don inganta rayuwar al’ummarsa ba. Hasalima na ji El-Rusau na cewa Man kaza na Bayan Kada ya salwantar da Hauro gashin balama dari manuniyar sama.
Saboda haka, akwai bukatar mu bijiro wa Gwamna Mai sunan sulalla da tambaya, kan cewa tsakanin Malam Nasara El-Rusau da Man kaza na Bayan Kada wa ya fi kimar daraja da basirar tarairayar harkokin al’umma? Kuma Man kaza har maganadisu ya kafa don ya kama al’umma, amma har yanzu bai cafko komai ba. Lallai akwai gyara a kan wnanan mayen karfe, mai kokarin yi wa al’umma karfa-karafa a zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje.
Shi kuwa Gwamna Birnin Dabo, ba sai na bijiro maka da dimbin aikace-aikacen da ya kwantsama ba, tunda nasan ka baje na-mujiyarka, ka sha kallo. Ya kuma aiwatar da wadannan aikace-aikace ne, a daidai lokacin da kake tsuwurwurta aika-aikar sulallewa da sulallan al’umma. Kuma kamar yadda na bayyana a makon da ya arce, ’yan lelenka na fuskantar tuhumar sulalelewa da sulallan al’umma da kuma yi wa al’umma kisan gilla. Gwamna mai sunan sulalla, wanne ne ba wanne ne ba?
Uwa-uba, jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ita ta yi wa kanta zagon kasa, har ma da na sama, inda ta yi ta tadiye ’ya’yanta. Yau sanin kowa ne, cewa, tsohon mai karanta Labaran Mako a fadar Shugaban kasa, Gudun-loko da Jona-tantin mulki, ya koma jam’iyya mai zakara, saboda mai dan boto ta jirga shi, ta hana shi takara. Babbar shaida kan cewa mai dan boto ita ta kassara kanta da kanta, shi ne, kalaman d aaka ji Dumu-dumu Muzu-muzu ya furta a wajen kaddamar da yakin neman zabi-sonka, inda ya kasa kannewa, har ya ce da Shugaban Gudun-loko, lallai sai an tabbatar da adala, sannan jam’iyyar za ta samu kimar daraja a wajen al’umma.
Batu na ingarman karfe, mai da boto ta shafe shekaru sili da babban lauje tana jan ragamar al’ummar kasar nan, amma babu abin da ta aiwatar illa tsarin tsimi da ta’adi: samartakar kusu da lukudi; ga zaman-takewa, wato kashin shakushe; da damo-da-kura-da-diyya, a wasan Samson-siya-siya da kwanyar al’umma, bisa tafarkin dama-dama-da-kurda-kurda.
Gwamna mai sunan sulalla na tabatar kana sane da aika-aikar da jam’iyyarka ta tafka, inda ta karke da ta’asa a kwanon tasarta. Ga shi saboda tabewar basira, wai jam’iyyarku ta dauko Fufffuken-fankan-fayau, ya jagoranci yakin neman zabi-sonka. Wannan mugun daji ba dan goyo ba ne. domin sanin kowa ne yana fuskantar tuhuma a Hukumar Gwagwarmaya da Arangama da masu fashi da mukami ko da dabara. Domin ta’asar da ya tafka, tana nan a rubuce. Sai ku tuntubi Mace Mai fari-da-idanu ko Loma-a-murde, duk da cewa kun murde shi, har ya zama muzurun lami.
Lallai lokaci ya yi da daukacin masu karatun wasikar auran-dawa da na gida irin na Gwmana mai sunan sulalla za su fasko cewa, talken tuwonsu ya daina sulala, balantana su sulale da sulallan al’umma. A yi saurin ingiza keyarsu, su tafi su yi na kasa, don kada su kasa, mu kuwa mu kasa mu kwashi kashi. Mai sunan sulalla dai ‘ba ka ga tsuntsu, ba ka ga tarko.’ Domin daukacin wadanda kake dura wa ashariya, sun fi ka kimar darajar mutumtaka a wajen al’ummar Haurobiya.
Mutanen Jihar Jijjiga-ciyawa kada ku yarda a kakaba muku Rungumar rigima. Jama’ar Kazauna-a-zaure ku zurare daga salon tafiyar mai karfa-karafa. Ina jama’ar Ja-hade, ku janye kada ku hade da shi. Turakin hawan sa ne ya mika masa jihar, da ma bai taba samun galaba a zabi-sonka ba. Lallai a wancakalar da shi, ta yadda zai fara laluluben sulallan sulalelewa daga kasar Haurobiya. Dama gara a cire mana bara-gurbi.