Da Dumi Dumi

Gwamna ya ja kunnen mutanen kauyen  Kishi kan hana jami’an Kwastam yin aiki

Kanar Hameed Ali Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa
Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali

Hukumar Kwatsam ta yaba wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan hanzarta tsawatar wa al’ummar kauyen Kishi game da hana jami’an Kwastam gudanar da aiki a cikin kauyen da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin.

Kwanturolan Hukumar Kwastam a jihohin Oyo da Osun, Abdullahi Zulkifili ne ya yi wannan yabo a wajen taron ’yan jarida a ofishinsa a Ibadan. Ya ce “Lokacin da na kai wa Gwamna Seyi Makinde ziyarar ban-girma a ofishinsa, na sanar da shi halin da jami’an Kwastam suka samu kansu a shekarun baya inda al’ummar garin Kishi suka ki amincewa mu shiga garin domin gudanar da ayyukanmu. Ba tare da bata lokaci ba Gwamnan ya tsawata wa al’ummar garin kan illar da za su janyo wa kansu muddin suka ci gaba da daukar wannan mataki.”

Ya ce “Dattawa da masu ruwa-da-tsaki a karkashin jagorancin Sarkin Kishi sun amsa kiran Gwamnan inda suka yi mana maraba lokacin da na jagoranci jami’an tsaro don ziyartar garin.” Kwanturola Zulkifili ya ce “Sarkin Kishi ya nuna nadama kan abubuwan da suka auku a baya, inda ya tabbatar musu da cewa hakan ba zai sake aukuwa a gaba ba. “Domin tabbatar da wannan bayani, Sarkin ya nuna mana wasu gidaje da ya ce al’ummarsa ne suka bayar kyauta a matsayin ofishin aiki da wurin kwana na tsawon wata uku mu yi amfani da su. Wannan ya sa muke jinjina wa Gwamna Makinde kan daukar matakin gyara wannan al’amari da ya zama barana ga tattalin arziki,” inji shi.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa ana zargin da yawa daga cikin mutanen garin Kishi sun dogara da ayyukan fasa kwauri ne kasancewar garin na kusa da kan iyakar da kasar Benin.  Hakan ne ya sa su hana jami’an Kwastam shiga cikin garin.

ADVERTISEMENT
Share