✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Zulum ya kai ziyarar wuni biyu a Bama

Gwamanan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a garin Bama, wanda ya taba zama hedikwatar Boko Haram. Gwamnan…

Gwamanan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a garin Bama, wanda ya taba zama hedikwatar Boko Haram. Gwamnan ya raba wa magidanta dubu 12 da 887 tallafin kayan abinci, sannan ya duba wasu makarantun firamare da karamar sakandare da Boko Haram suka kone da aka sake gina su.

Gwamna Zulum ya nuna bacin ransa kan yadda malamai ba sa zuwa aiki, kuma ya yi alkawarin daukar mataki domin ya zama darasi ga wadansu.

Sauran wuraren da Gwamna Zulum ya ziyarta a garin Bama sun hada da Kwalejin Ilimi ta Umar El-Kanemi, wadda ita ma Boko Haram suka kona, sai Makarantar Sakandaren Je-Ka-Ka-Dawo, da kuma masaukin baki na Indimi.

Tuni Gwamna Zulum ya ba da umarnin a fara karatu a Kwalejin Ilimi ta Umar El-Kanemi a zangon karatun badi, sannan ya ba al’ummar kauyen Soye tabbacin za a gina musu garinsu da Boko Haram suka kona, domin su koma garinsu.

Gwamna Zulum ya kuma ba da umarnin daga darajar wasu makarantun firamare biyu zuwa manyan makarantun sakandare. A daya daga cikin makarantun firamaren da Gwamnan ya ziyarta ya ba wadansu ’yan mata biyu gurbin karatu, domin sadaukar da kansu da suka yi wajen koyar da dalibai.

Gwamna  Zulum ya kai irin wannan ziyara a Rann a Karamar Hukumar Kalabalge, inda a can ma ya rarraba kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijira.