✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Bauchi yana jinya a asibitin Landan

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, yana jinyar rashin lafiya a birnin Landan. Babban mai taimakawa Gwamnan akan watsa labarai Mukhtar Gidado, ne ya…

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, yana jinyar rashin lafiya a birnin Landan.

Babban mai taimakawa Gwamnan akan watsa labarai Mukhtar Gidado, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Bauchi sai sanarwar bata bayyana abin da ke damun Gwamnan ba.

Gwamnan ya mika sakonsa ga jama’ar jihar daga gadon asibitin, yayin da kotun koli zata ci gaba da sauraren karar zaben Gwamnan jihar da aka shigar don yanke hukunci.

Sakon Gwamnan jihar na cewa, “ A yanzu haka ina asibitin Landan, ina fatan Allah zai bamu nasara a wannan karar da aka shigar gaban kotun koli, da yardar Allah nasara ta mu ce.”