✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Osun ya jagoranci tattakin bikin al’ada na Osun Osogbo

A karshen makon jiya ne Gwamna Gboyega Oyetola, na Jihar Osun ya jagoranci dimbin ’yan asalin jihar suka tattaki mai tsawo a garin Osogbo domin…

A karshen makon jiya ne Gwamna Gboyega Oyetola, na Jihar Osun ya jagoranci dimbin ’yan asalin jihar suka tattaki mai tsawo a garin Osogbo domin girmama bukukuwan al’ada na ‘Osun Osogbo Carnibal’ na bana da za a shafe kwana 11 ana yi.                                                                                                                                                     An saba yin wannan biki a garin Osogbo hedkwatar Jihar Osun a daidai wannan lokaci a kowace shekara domin tunawa da tushen kabilar Yarbawa (Odua) tare da  yin wasanni da nune-nunen kayan al’adun gargajiya.

An kada gangar fara doguwar tafiyar ce daga kan hanyar Better Life zuwa Ahmadiyya da Mararrabar Oja-Oba aka ratsa ta Obate zuwa Marabar Sabo aka wuce zuwa Balogun Agoro zuwa Isale Aro da Jolayemi zuwa Isale Osun aka kare a fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji.

A jawabinsa a fadar Ataoja na Osogbo bayan kammala tattakin,  Gwamna Oyetola ya ce gwamnatin jihar ta yi tanadin isassun jami’an tsaro da za su yi aikin sa-ido da lura da kai kawon jama’a domin tsaron mahalarta bikin na ciki da wajen Najeriya. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukaka martabar wannan biki ta fannin gayyatar manyan baki daga kasashen duniya domin su kashe kwakwatar ido a wajen bikin da ake sa ran zai samar da wuraren yawon bude-ido da kuma kudaden shiga ga gwamnatin.

Gwamnan wanda Dokta Obawale Adebisi na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Al’adu da Yawon Shakatawa, ya wakilta ya ce, gwamnati ta riga ta samar da wani sabon tsari na yawon bude-ido mai suna “Karaole Odua” da za a yi amfani da shi wajen janyo hankalin ’yan asalin jihar su dawo gida daga kasashen Turai domin gane wa idonsu asalin tarihinsu. Ya ce, “Burinmu shi ne mu yi kyakkyawan shiri  da zai taimaka wajen karkato da hankalin Yarbawa musamman ’yan asalin jihar nan su dawo gida a tsakanin ranar 10  zuwa 21 ga watan Agustan kowace shekara. Ana samun miliyoyin Naira a wajen gudanar da irin wannan biki a kowace shekara duk da yake ba dukkan kudin ne suke shiga aljihun gwamnati ba.”

Gwamnan ya ce hakan ne ya sa aka bullo da sabon tsarin da gwamnati za ta yi amfani da shi wajen samun kudin shiga.

Da yake maraba da mutanen da suka yi tattakin a fadarsa Ataoja na Osogbo Oba Jimoh Oyetunji ya ce tunatar da ’yan asalin jihar ne cewa a baya an saba kada kararrawar fara wannan biki ne da  share kazanta a garin Osogbo da ake yi wa lakabi da ‘Wopopo’ a Yarbance, inda ’yan asalin garin Osogbo da hadin gwiwar masu yawon shakatawa suke sadaukar da kai wajen yin irin share garin, amma a bana aka kara da yin doguwar tattaki a kasa domin tabbatar da dawo da martaba da inganta bikin na ‘Osun Osogbo’ wanda Hukumar Raya Al’adu da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta taimaka wajen sanya sunan bikin mai tarihi a cikin taswirarta don karkato da hankalin duniya gare shi.